Bayan da aka rufe zama na 3 na gasar wasannin Olympic a shekarar 1904, ana iya cewa, a kwana a tashi, tasirin wasannin Olympic ya kara habaka, kuma abu mai ban sha'awa shi ne an taba shirya wata kwarya-kwaryar gasar wasannin Olympic a birnin Athens na kasar Greece a shekarar 1906 wato bayan zama na uku na gasar, amma kafin zama na hudu.
A tarihin gasar wasannin Olympic, an taba mayar da ita bikin baje koli na duniya, alal misali, gasar wasannin Olympic ta Paris na kasar Faransa da gasar wasannin Olympic ta St. Louis na kasar Amurka. Amma jama'ar kasar Greece suna ganin cewa, gasar wasannin Olympic ita ce alamar wayin kai ta kasarsu, muddin dai an nace ga tunanin nan, to, za a kiyaye tunanin gargajiyar wasannin Olympic. Saboda haka, mutanen kasar Greece sun gabatar da roko biyu ga Coubertin, daya daga cikinsu shi ne a shirya wata cikakkiyar gasar wasannin Olympic a Athens a shekarar 1906 don taya murnar cikon shekaru 10 da aka farfado da wasannin Olympic, na biyu shi ne suna fatan za a zabi Athens ya zama wuri daya kadai inda za a shirya gasar wasannin Olympic har abada.
Coubertin bai yarda da roko na biyu ba, ya ce kamata ya yi a ci gaba da shirya gasar wasannin Olympic a wurare daban daban na duniya. Amma ya yarda a shirya wani sabon zama na gasar wasannin Olympic a Athens a shekarar 1906. Kasar Greece ta mayar da wannan zama na gasar 'zama na biyu na gasar wasannin Olympic ta duniya', a bayyane ne kasar Greece ta yi na'am da gasar wasannin Olympic ta shekarar 1896 kawai wato ba ta yi na'am da sauran gasannin ba. Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 1896 ya ci gaba da aikinsu, kuma filin wasannin motsa jiki da aka gina kafin shekaru 10 da suka shige yana da kyau, shi ya sa ana iya ci gaba da yin amfani da shi, ban da wannan kuma, sun samu kudi ta hanyar sayar da kan sarki kamar yadda suka yi a da. Shi ya sa aikin shirya gasar yana tafiya lami lafiya, kuma tasirin gasar shi ma ya fi girma.
Musamman ga 'yan wasa daga kasashen Turai, sun yi farin ciki kwarai da gaske saboda ba su shiga gasar ba shekaru da yawa da suka wuce. A karshe dai, gaba daya 'yan wasa 884 da suka zo daga kasashe fiye da 20 sun halarci gasar, wadanda a cikinsu akwai 'yan wasa mata 7.
Abun burgewa shi ne a gun wannan gasa, a karo na farko ne 'yan wasa daga kasar Masar ta Afirka da kasar Turkey ta Asiya suka shiga gasannin da aka shirya, wato a karo na farko a tarihin gasar wasannin Olympic, 'yan wasa daga nahiyoyi biyar sun yi gasa tare.(Jamila Zhou)
|