Yau da shekaru 7 da suka gabata, lokacin da kasar Sin take neman izinin shirya gasar wasannin Olympics, birnin Beijing ya yi wa sauran kasashen duniya alkawarin cewa, zai shirya wata gasar wasannin Olympics mai inganci da ke nuna halayen musamman. Bayan wadannan shekaru 7, lokacin da ake kidaya 'yan kwanaki 30 da gasar wasannin Olympics ta Beijing, tare da hakikanan matakai ne, birnin Beijing ya shaida cewa, tabbas ne zai cika alkawarinsa, kuma zai gabatar da wata amsar da za ta samu amincewa daga duk duniya.
Bisa alkawarin da birnin Beijing ya dauka, halayen musamman da za a nuna a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing su ne, al'adun kasar Sin da al'adun da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum da halin zamani da ake ciki yanzu da yadda fararen hula suke halartar gasar. A cikin wadannan shekaru 7 da suka gabata, lokacin da ake share fagen gasar, ana nuna wadannan halayen musamman a duk fannoni, kamar a lokacin da ake zana "Fuwa", wato abun fatan alheri na gasar wasannin Olympics ta Beijing da "Gajimare mai kawo fatan alheri", wato yolar gasar da filin wasa na kasar Sin, wato "Shekar Tuntsu" da dakin ninkaya, wato "Water Cubic", an sanya al'adun kasar Sin a cikinsu. Yanzu sun riga sun zama alamun da ke bayyana wa sauran kasashen duniya al'adun kasar Sin.
A waje daya kuma, ana nuna al'adun da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum a wurare da yawa. Bikin nuna al'adun wasannin Olympics na shekara ta 2008 da aka soma yi a karo na 6 a nan birnin Beijing tun daga ran 23 ga watan Yuni, yana bayyana yadda ake hada ruhun wasannin motsa jiki da al'adu, kuma da ruhun wasannin Olympics da al'adun kasar Sin, kuma ana nuna al'adu iri daban daban a gun bikin.
Bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofarta ga kasashen waje da shekaru 30 da suka gabata, kasar sin ta samu sauye-sauye sosai daga dukkan fannoni. Bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing da ake kiran shi "ziyarar da ke bayyana ruhun jituwa", ba ma kawai ana bayyana tunanin "tabbatar da zaman lafiya da sada zumunta da neman cigaba" ba, har ma ana bayyana yadda Sinawa suke kokarin neman cigaba. Bugu da kari kuma, a lokacin da ake neman alama da abun fatan alheri da wakoki na gasar, kuma a lokacin da ake daukar mutane masu aikin sa kai da mutane masu yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijng, ana bayyana yadda ake sa kaimi ga dukkan jama'ar duniya da su halarci ayyukan gasar.
Bugu da kari kuma, bisa alkawarin da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ya dauka, za a shirya wata gasar wasannin Olympics mai inganci. Wannan inganci yana shafar fannoni 8, kamar su, filaye da dakunan motsa jiki da aikin shirya gasanni da bikin kaddamar da gasar da bukukuwan al'adu da ba da hidima ga kafofin watsa labaru da ayyukan tsaron gasar da masu aikin sa kai da ayyukan da ke shafar zirga-zirga da zaman rayuwar 'yan wasa da sakamakon gasanni da yadda za a nuna wa kasashen duniya wani kyakkyawan birnin Beijing mai wayin kai. A cikin shekaru 7 da suka gabata, ana shirya ayyukan gasar bisa shirin da aka tsara kamar yadda ya kamata domin tabbatar da ganin an shirya wata gasar wasannin Olympics mai inganci.
Jama'a masu sauraro, gasar wasannin Olympics wani kasaitaccen biki ne ga dukkan membobin kwamitin Olympics. Shirya wata gasar wasannin Olympics mai inganci da ke nuna halayen musamman, ba ma kawai alkawari ne da jama'ar kasar Sin suka dauka ba, har ma buri ne da jama'ar duk duniya suke neman cimmawa. Birnin Beijing zai yi maraba da zuwan abokai na nahiyoyi 5 na duniya da hannu biyu biyu.
|