Masu sauraro, wakilinmu ya samu wannan amo ne daga wani darasin wasan kwaikwayo na waka na kasar Sin wato Pekin Opera da ake koyarwa a makarantar firamare ta titin Xiangjiang ta birnin Tianjin na kasar Sin. Tare da kide-kiden wasan Peking Opera da ake watsa a cikin na'urar daukar murya, Pan Xiaotong, wata 'yar makaranta tana yin wasan Peking Opera bisa jagorancin malami. Kuma ta gaya wa wakilinmu cewa, ta riga ta koyi wasan Peking Opera har shekaru fiye da biyu. Kuma ta kara da cewa, "A ganina, yin wasan Peking Opera yana da ban sha'awa, kuma ina sha'awar kalmomin waka da ake rerawa a cikin wasan. Kafin mu koyi wasan Peking Opera, kullum malam Fan ya kan gaya mana wasu labarai game da wasan, ta haka za mu iya kara fahimtarsa da kuma koyonsa yadda ya kamata."
Kullum a kan kira birnin Tianjin "garin wasannin kwaikwayo na waka na kasar Sin", inda ake iya samun tushen fararen hula mai inganci na wasan Peking Opera. Yau da shekaru da dama da suka gabata, bi da bi makarantun firamare da sakandare da dama sun kaddamar da shigad da wasan Peking Opera cikin darussan koyar da wake-wake. A shekara ta 2005, makarantar firamare ta titin Xiangjiang ta birnin Tianjin ta tattara malamai wajen tsara littattafan koyar da wasan Peking Opera, da kuma kaddamar da ayyukan koyar da wasan. Yanzu ba kawai 'yan makarantar suna iya bayyana ilmi game da wasan ba, har ma suna iya rera wasu wakokin da ke cikin wasannin Peking Opera. Yang Qiuyue, wata malamar koyar da wake-wake ta bayyana cewa, "Game da yaran da suka fara karatu ba da jimawa ba, wannan shi ne karo na farko da su san wasan Peking Opera, shi ya sa da farko muka yi amfani da wasu na'urorin zamani na koyarwa kamar bidiyo domin kara sha'awar da suka nuna wa wasan sannu a hankali."
1 2
|