Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-08 16:45:25    
Bunkasuwar tattalin arzikin Afirka tana fuskantar kalubale daga fannoni da yawa

cri

Bunkasuwar tattalin arzikin Afirka tana fuskantar kalubale daga fannoni da yawa sabo da hauhawar farashin hatsi da abubuwan konawa a kasuwannin kasashen duniya, da karancin wutar lantarki da kuma raguwar darajar kudi.

Bisa rahoton da aka bayar a gun dandalin tattalin arzikin duniya game da kalubalen Afirka an ce, daga cikin kasashe 86 na duk duniya wadanda suke samun kudin shiga kalilan da karancin abinci, da akwai rabinsu na kasashen Afirka ne. Kasashen Afirka ciki har da Mozambique da Kenya da Mauritaniya da Bourkina Faso da Kamaru dukkansu sun gumu da tashin hankali a wannan shekara sabo da hauhawar farashin hatsi.

Kwanan baya, karamar kungiyar samun ci gaban Afirka wadda take hade da shahararrun mutane 11 ciki har da tsohon babban sakataren MDD Mr. Kofi Annan, da tsohon shugaba Tony Blair na kasar Ingila, da tsohon manajan direktan kungiyar asusun kudin kasashen duniya ta bayar da wani rahoto mai lakabin "Alkawari da makoma game da bunkasuwar Afirka". Rahoton ya bayyana cewa, matsalar abincin duniya tana nan tana kara jawo barazana ga ci gaban tattalin arzikin da Afirka ta samu bayan kokarin da ta yi cikin shekaru da yawa, ya kamata kasashen duniya su dauki matakai domin kara samar da hatsi da yawa ga kasuwannin kasashen duniya, kuma su kara ba da babban taimakon kudi ga hukumomin kasashen duniya da abin ya shafa da gwamnatocin kasashe wadanda suke fama da karancin abinci, ta yadda za a kawar da mugun tasirin da ake jawo wa Afirka sabo da hauhawar farashin abinci a duniya.

A sa'i daya kuma, bisa ci gaban da Afirka ta samu cikin 'yan shekarun da suka wuce wajen tattalin arziki, bukatar da kasashe daban-daban suke yi a fannin wutar lantarka tana ta karuwa sosai. Kasar Afirka ta kudu kasa ce mafi girma wajen samar da wutar lantarki, ta taba fitar da wutar lantarki ga kasashen da ke makwabtaka da ita cikin dogon lokaci, amma yanzu yawan wutar lantarki da ta fitar bai ishe ta ita kanta ba, shi ya sa bunkasuwar tattalin arziki na kasar tana gamuwa da babban kalubale sabo da karancin wutar lantarki, haka kuma yana daurin talala ga kara samun bunkasuwar tattalin arzikin duk Afirka baki daya.

Ban da wannan kuma, matsin lambar da ake yi wa kasashen Afirka sabo da raguwar darajar kudi yana ta karuwa a kowace rana, wannan ya zama babban hani a bayyane ga samun karuwar tattalin arziki.

Sabo da mugun tasirin tsawwalar farashin hatsi, shi yasa yawan kudin da mazaunan kasar Afirka ta kudu suka kashe domin sayen kaya a watan Afril da ya wuce ya karu da kashi 10.4 bisa 100. Masanan tattalin arziki sun kimanta cewa, yawan raguwar darajar kudi da aka samu a Afirka ta kudu ba zai samu kyautatuwa ba wato zai hau sama har zuwa kashi 3 zuwa 6 cikin 100 bisa ma'aunin da gwamnatin kasar ta tsayar cikin shekaru 2 masu zuwa. Yawan raguwar darajar kudin da kasar Angola wadda take babbar kasa wajen fitar da man fetur a Afirka ta samu a watan Mayu na wannan shekara ya kai kashi 12.03 bisa 100, wato ya kai matsayin koli tun daga watan Oktoba na shekarar da ta wuce zuwa yanzu.

Bisa sakamakon kididdigar da gwamnatin Afirka ta kudu ta bayar kwanan baya an ce, ko da yake Afirka ta kudu, kasa ce mafi karfi wajen tattalin arziki wadda kullum take ba da jagoranci wajen bunkasa tattalin arzikin Afirka, amma sabo da tsawwalar farashin abinci da makamashi, shi ya sa daga watan Janairu na wannan shekara, matsakaicin yawan farashin muhimman abinci ciki har da shinkafa da garin alkama da man girki ya karu da da kusan kashi 25 bisa l00. (Umaru)