
A ran 8 ga wata, an kammala mika wutar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Huhehaote, hedkwatar lardin Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta cikin nasara.

Dukan tsawon hanyar da ake bi wajen mika wutar ya kai kilomita 6.2, yawan jama'ar da suka dauki wutar yola ya kai 208. An yi bikin fara mika wutar a filin Baoding na dakunan nune-nune na lardin Mogoliya ta gida. Shahararen dan wasan kwallon kwando na kasar Sin Mr.Mengke Bateer ya dauki wutar yola ta farko da aka mika a birnin Huhehaote. A lokacin mika wutar an bi ta cibiyar nune-nune da tarurruka da titin Tengfei da sauran wurare, wurin karshe an kai wutar filin Ruyi. Shahararriya mai nuna sinima Si Qingaowa ta dauki wutar yola ta karshe.
Bayan an kammala mika wutar a birnin Huhehaote, za a mika wutar wasannin Olympic ta Beijing a biraren E'erduosi da Baotou na lardin Mongoliya ta gida.(Abubakar)
|