Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-07 15:23:36    
An sake samu fashewar bom na kunar bakin wake a babban birnin kasar Pakistan

cri

Da misalin karfe 8 da dare na wannan rana, 'dan kunar bakin wake ya tada bom a gaban wata hukumar 'yan sada da ke dab da masallacin 'Lal Masjid', inda yake da 'yan sanda fiye da 20. Abun lura shi ne, nisan wurin da aka tada bom da masallacin 'Lal Masjid' ya kai mitoci dari kawai, kafin mintoci 15 na fashewar bam, mutane da yawa sun gama tarurrukansu a wurin. Masu halartar tarurrukan sun fadi cewa, ya kamata shugaban kasar Pakistan Mr. Musharraf da kuma ministan harkokin gida na lokacin wato Mr. Aftab Sherpao su sauke nauyin da ke bisa wuyansu kan lamarin 'Lal Masjid' a shekarar da ta wuce, haka kuma sun gaya wa kasar Amurka cewa, ba za a daina yin Jihad ba, mutane da yawa sun yi ruri da yin ramuwar gayya.

Ko da yake a halin yanzu, ba a iya tabbatar da cewa, ko wannan lamarin fashewar bam yana da nasaba da tarurrukan ko a'a, amma kafofin watsa labarai suna ganin cewa, mai yiyuwa ne wannan lamarin fashewar bom na kunar bakin wake shi ne ramuwar gayya da aka gudana, makasudinsa shi ne domin nuna ra'ayinsu ga gwamnatin kasar Pakistan, da kuma adawa da lamarin 'Lal Masjid' da ya faru a shekarar da ta wuce.

A sa'i daya kuma, kafofin watsa labaru suna ganin cewa, ban da lamarin 'Lal Masjid' da ya faru a shekarar da ta wuce, mai yiyuwa ne fashewar bam tana da nasaba kai tsaye da matakan soja da aka dauka a tsakanin rundunonin tsaro na kasar Pakistan da dakarun Taliban da ke arewa maso yammacin kasar Pakistan.(Danladi)


1 2