Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-07 14:18:35    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Mun sami labari kwanan baya cewa, cikin shekarar da muke ciki jihar Tibet za ta mai da hukumomin kauyuka a matsayin tushe don bude dakunan littattafai cikin gidajen manoma 660 a makekun yankunan noma da na kiwon dabbobi da ke jihar, ta yadda za a daidaita matsalolin da manoma da makiyaya ke gamuwa da su wajen saye da yin aro da kuma karanta littattafai.

Mr. Wangdu Tsering, shugaban hukumar ba da labaru da buga littattafai na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, a makekun yankunan noma da na kiwon dabbobi na jihar Tibet, manoma da makiyaya sun yi karancin abubuwa sosai wajen tunani da al'adu. Aikin bude dakunan littattafai cikin gidajen manoma yana da muhimmiyar ma'ana ga yadada al'adu masu ci gaba da fadakar da dimbin manoma da makiyaya wajen ilmin kimiyya da fasaha.

An ce, za a ajiye littattafai da yawansu fiye da 1000 da mujallu fiye da nau'o'i 30 cikin kowane dakin littattafai, daga cikin su har da littattafai da mujallu da aka buga domin ba da taimako ga manoma da makiyaya da su kubutar da kansu daga talauci ta hanyar kimiyya da fasaha da ba da ilmi da kiwon lafiya.

---- Kwanan baya, yara 84 na kabilar Qiang wadanda suka zo daga gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan inda girgizar kasa ta shafa sun je sansanin tsaron iyakar kasa dake birnin Shenzhen na kasar Sin, kuma za su shafe watanni 3 ko fiye suna yin karatu a nan har zuwa ranar da za a kammala aikin gina makaranta a garinsu.

An ce, wadannan yara 'yan kabilar Qiang su 'yan makaranta ne masu talauci wadanda suka zo daga aji na farko har zuwa na 6 na wata makarantar firamare da ke gundumar Wenchuan, a lokacin da suke karatu a sansanin soja na runduna ta 7 na tsaron bakin iyakar kasa dake lardin Guangdong, rundunar soja da kungiyar nuna jin kai ta birnin Shenzhen za su yi kokarin samun malaman koyarwa na makarantun firamare da na sakandare na birnin da kwararrun hukamar tallafin mutane masu fama da bala'in ilmin halin dan Adam musamman domin ba da taimako ga wadannan yara.

Yanzu yawan mutane 'yan kabilar Qiang ya wuce dubu 400 a kasar Sin, wadanda yawancinsu suke zama a gundumomin Mao da Wenchuan da Li da Beichuan, dukkan wadannan wurare suna cibiyar girgizar kasa da ta auku a wannan gami, shi ya sa ba ma kawai an sami matukar hasarar rayuka da haddasa raunuka ba, hatta ma an jawo illa sosai ga al'adun kabilar Qiang wajen dukiyoyi.