Tun daga shekarun 1980, 'yan kasuwa na Taiwan da yawa sun fara zuwa babban yankin kasar Sin don zuba jari da yin sauran harkokin kasuwanci, kuma sun sami riba mai tsoka a sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin babban yankin kasar cikin sauri. Malam Chen Fengrong yana daya daga cikinsu. Shi babban direkta ne na babban kamfani mai suna Quantong na Taiwan, kuma kakanninsa sun fito ne daga birnin Quanzhou na lardin Fujian da ke a bakin teku na kudu maso gabashin kasar Sin. Bayan da ya yi bincike a birnin Guangzhou na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin a shekarar 1986, sai ya yanke shawara kan zuba jari a birnin. Kuma a shekarar 1988, ya gina kwata a tashar jiragen ruwa mai suna Huangpu ta birnin Guangzhou, don aiwatar da harkokin sufuri.
Da Malam Chen ya waiwayi hanyar da ya bi wajen zuba jari a babban yankin kasar Sin, sai ya bayyana cewa, ya taba gamu da batutuwa da yawa, a lokacin da ya fara zuba jari a babban yankin kasar a wadancan shekaru, amma ya daidaita su bisa taimakon da ya samu daga wajen hukumomin birnin da kuma sauran hukumomin da abin ya shafa. Ya kara da cewa, "a hakika dai, a farkon lokacin da muka fara gudanar da harkokin kasuwanci a birnin Guangzhou, mun sami babban taimako daga wajen kananan hukumomi da gwamnatin birnin a fannoni daban daban. Mun ci gajiyar manufofin da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa game da nuna gatanci ga 'yan kasuwa na Taiwan."
Bisa irin wannan taimakon da ya samu, Malam Chen Fengrong ya fara samun ci gaba wajen bunkasa harkokinsa cikin sauri. Yanzu, ban da kwatar tashar jiragen ruwa, kuma ya kafa kamfanin ciniki don gudanar da harkokin cinikayya a tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan. Ka zalika ya kafa wani sansanin kiwon kifaye. Bisa yarjejeniyoyin da aka daddale a tsakanin sansaninsa da manoma, Malam Chen yana samar wa manoma da kananan kifaye don kiwonsu, sa'an nan kuma zai sayi manyan kifayen da manoma suka yi kiwonsu.
Yanzu, yawan kananan kifayen da sansaninsa ke samarwa ya kan kai miliyan 50 a ko wace shekara. Da malam Chen ya tabo magana a kan sansaninsa, sai ya ce, "yanzu ana cinikayyar kifaye sosai a lardin Guangdong. Kifayen da ake sayarwa daga lardin zuwa kasashen waje su kan yi yawa a ko wace shekara, kuma ana samun karancin kifayen da ake bukata. Sabo da haka muna jawo kananan kifaye mafi kyau daga Taiwan don kiwonsu a lardin."
Malam Chen ya kara da cewa, yayin da sansaninsa ke samar da kananan kifaye ga manoma, kuma yana koyar musu fasahar kiwonsu. Yana kuma fatan nan gaba zai hada kansa da kauyuka da garuruwa wajen kafa wurare masu gwada fasaha ta yadda za a kara jagorancin manoma wajen kiwon kifaye ta hanyar zamani.
Da Malam Chen ya tabo magana a kan bunkasuwar tattalin arzikin babban yankin kasar Sin, sai ya nuna imani sosai cewa, "birnin Guangzhou da na Shenzhen da Shanghai da sauransu sun sami ci gaba sosai da za a zo a gani. Ko nan da shekaru goma zuwa 15, ko shakka babu, babban yankin kasar zai ci gaba da samun bunkasuwa. A hakika, muna sa ran alheri ga bunkasuwar tattalin arzikin babban yankin kasasar a nan gaba, sabo da haka mun bayyana wa 'ya'yanmu cewa, ya kamata, su ma su gudanar da harkokinsu a babban yankin kasar, kuma muna fatan za su gudanar da harkokinsu da kyau a nan gaba, amma yanzu ma suna gudanar da harkokinsu da kyau."
A sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin babban yankin kasar Sin cikin sauri, 'yan kasuwa na Taiwan da ke gudanar da harkokinsu da zamansu a babban yankin kasar zasu karu sosai. Kuma za su yi amfani da babbar damar da suke samu wajen bunkasa harkokinsu a babban yankin kasar Sin.(Halilu)
|