Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-07 09:48:54    
An fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Lanzhou

cri

Yau 7 ga wata, an fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Lanzhou da ke lardin Gansu a arewa maso yammacin kasar Sin.

Da misali karfe 8 na safe, an fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a dandalin gadar Zhongshan ta kudu da ke birnin Lanzhou, mai dauke da wuta na farko shi ne jarumi wajen yaki da bala'in girgizar kasa Tian Yu. Daga bisani kuma, za a bi hanyoyin da za su iya bayyana halin da ake ciki a Rawayen kogi da ke kan hanyar Binhe ta arewa da ta kudu a birnin Lanzhou, a kan hanyoyin mika wutar gasar wasannin Olympic za a bi unguwanni 3 watau Chengguan da Qilihe da Anning, a karshe dai za a isa wurin shakatawa na bajen injuna masu ban ruwan na gargajiya da ke birnin Lanzhou, tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar wasannin Olympic ta Beijing zai kai kilomita 27, masu dauke da wuta su 296 za su shiga cikin wannan bikin.

A sakamakon yankin Longnan da ke lardin Gansu yana daya daga cikin yankunan da suka fi fama da bala'in girgizar kasa da ya fadawa gundumar Wenchuan a ranar 12 ga watan Mayu, sabo da haka, bikin mika wuta a lardin Gansu ya sanya yaki da bala'in girgizar kasa don ya zama babban take wajen mika wutar wasannin Olympic, haka kuma ya hada da bikin mika wutar wasannin Olympic da sake farfado da wurare da bala'in girgizar kasa ya shafa tare.(Bako)