|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-07-05 17:14:14
|
An samu nasarar yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Dunhuang
cri
Yau 5 ga wata, an samu nasarar yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Dunhuang na lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin.
Birnin Dunhuang zango ne na farko da za a yi yawo da fitilar a lardin Gansu. Tsawon hanyar da aka bi wajen bikin ya kai kusan kilomita 7.6, masu yawo da fitilar da yawansu ya kai 120 sun halarci bikin.
A ranar 6 ga wata kuma, za a cigaba da yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Jia Yuguan na lardin Gansu. (Bilkisu)
|
|
|