Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-04 21:01:45    
Mutane 69196 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa ta Wenchuan

cri
Bisa kididdigar da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar an ce, ya zuwa yau ranar 4 ga wata da tsakiyar rana, mutane 69196 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da mutane 18385 suka bace.

Ya zuwa ranar 4 ga wata, gwamnatoci bisa matakai daban daban na kasar Sin sun bayar da kudi kusan yuan biliyan 55 kan ayyukan yaki da bala'in da ceto mutane, da kuma sake raya yankuna masu fama da bala'in. Bayan haka kuma, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da darajarsu ta kai kusan yuan biliyan 56 daga bangarori daban daban na gida da na waje. (Bilkisu)