Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-04 20:33:53    
Kasashe mambobi na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai za su bayar da taimako kan ayyukan tsaron wasannin Olympics na Beijing

cri
A gun taro a karo na 12 na majalisar hukumomin yaki da ta'addanci na shiyya-shiyya na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, wadda aka rufe a yau 4 ga wata a nan birnin Beijing, an bayar da wata sanarwar bayan taro, inda bangarorin kasashe daban daban suka yi alkawarin cewa, za su karfafa hadin gwiwarsu, don taimaka wa kasar Sin kan ayyukan tsaron wasannin Olympics na Beijing kamar yadda ya kamata, ta yadda za a tabbatar da samun nasarar shirya wasannin Olympics.

Bayan haka kuma, bisa sanarwar, bangarorin kasashe daban daban za su karfafa, da habaka hakikanan hadin gwiwarsu a fannin tsaron kai, bugu da kari kuma, za su dukufa wajen gina shiyyar tsakiyar Asiya da ta zama wata shiyya ta zaman lafiya mai dorewa, da samun wadatuwa tare, wannan ne kuma fata daya na kasashe mambobin kungiyar. (Bilkisu)