Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-04 17:52:14    
Kungiyoyin mazauna masu yawon shakatawa na karo na farko sun tashi daga babban yankin kasar Sin zuwa Taiwan

cri
Yau 4 ga wata an tabbatar da makasudin zirga-zirgar jiragen saman shata a karshen mako a tsakani gabobi 2 na mashigin teku na Taiwan, da yawon shakatawar da mazaunan babban yankin kasar Sin ke yi a Taiwan wanda kuma suke fatan yin sa tun da dadewa. Yau da safe kungiyoyin mazauna masu yawon shakatawa na karo na farko sun tashi daga nan birnin Beijing da sauran wuraren da ke babban yankin kasar Sin zuwa Taiwan ta jiragen saman aka yi shatarsu a karshen mako a tsakanin gabobi 2 na zirin tekun Taiwan.

Yawan mutanen da kungiyoyin mazauna masu yawon shakatawa na karo na farko ke kunshe da su ya wuce 7,000, wadanda suka je yankin Taiwan ne bayan da suka tashi daga biranen Guangzhou da Beijing da Nanjing da Xiamen da kuma Shanghai. Wadannan kungiyoyi masu yawon shakatawa za su kai ziyara ni'imomin wuraren ban sha'awa na Taiwan, tsawon lokacin ziyararsu kuma zai kai kwanaki 7 zuwa 10.

Mutane masu yawon shakatawa na babban yankin kasar Sin suna fatan kai ziyara a Taiwan sosai. Mr. Shi Anwei, mai yawon shakatawa na birnin Guangzhou ya bayyana cewa, "Wannan wani mafarki ne, ina fatan yin haka tun shekaru da yawa, amma a yau dai mun tabbatar da wannan makasudi, mun yi kamar ganawa da 'yanuwanmu wadanda kuma ba mu taba gamuwa da juna ba har shekaru gomai, ba zan manta da ranar yau ba har duk zaman rayuwata, haka ma ga kowanenmu, ina son zan dauki hotuna domin tunawa da wadannan lokutai masu daraja."

Mr. Shao Qiwei, shugaban hadaddiyar kungiyar yin mu'amala tsakanin gabobi 2 na zirin tekun Taiwan, kuma shugaban kungiyar mazauna masu yawon shakatawa ta karo na farko da ta tashi daga nan birnin Beijing ya bayyana cewa, "Mun amince cewa, bisa goyon bayan da jama'ar da ke gabobi 2 na zirin tekun Taiwan suke nunawa. da kokarin da sassan yawon shakatawa na gabobin 2 ke sanyawa, za mu iya kara gudanar da ayyukan yawon shakatawa da mazaunan babban yankin kasar Sin ke yi a Taiwan da kyau. Musamman ma za mu yi aiki da kyau tun daga farko, ta yadda za a aza harsashi mai inganci domin samun bunkasuwa a nan gaba."

Mr. Wang Yi, direktan ofishin kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na J.K.S. da na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ce, yau rana ce da ya kamata a tuna da ita cikin tarihin dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na zirin tekun Taiwan. Ya ce, "Ziyarar da mutane masu yawon shakatawa na babban yankin kasar Sin ke yi a Taiwan, da yin mu'amala tsakanin gabobin 2 wajen sadarwa da ciniki da zirga-zirgar jiragen sama, wannan ya zama babban yunkuri ne da ake yi, kuma fatan kowa ne, ba ma kawai jama'ar da ke gabobin 2 suke nuna maraba da hannu bibbiyu ba, kasashen duniya su ma suna jinjinawa sosai ga wannan aiki. Mutane masu yin ziyarar da ke cikin kungiyoyin mazauna masu yawon shakatawa na karo na farko na babban yankin kasar Sin dukkansu sun yi rajistar shiga wannan aiki ne bisa radin kansu, wadanda kuma suka zo daga gorabun aiki daban-daban, hanyoyin tarihin da suka bi kuma daban-daban ne, amma a yau sun taru a nan, suna yin fata iri daya, wato suna son isar da kyakkyawan zumuncin da jama'ar babban yankin kasar Sin ke nunawa 'yanuwanmu na Taiwan, sa'an nan kuma muna amince cewa, ba shakka 'yanuwanmu na Taiwan su ma za su nuna kyakkyawar maraba ga zuwan 'yanuwansu na babban yankin kasar Sin." (Umaru)