Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-04 16:21:19    
Kamfani na kasar Sin ya bayar da tikitocin jirgin sama ga yara masu koyon Sinanci na kasar Nijeriya don ba da taimako ga yaran da su je birnin Beijing don kallon gasar wasannin Olympics ta beijing

cri
A ran 2 ga wata, manajan ofishin kamfanin jiragen sama mai suna Nanfang na kasar Sin da ke a birnin Lagos Mr.Jiang Nan ya gayawa manema labaru cewa, a lokacin gasar Olympics ta kasar Beijing, kamfanin jiragen sama mai suna Nanfang zai bayar da tikitocin jirgin sama ga yara masu koyon Sinanci mafi kyau na kasar Nijeriya.

Ya bayyana cewa, domin kamfanin yana son kafa dangantaka mai kyau a tsakanin kamfanin da yankunan kasar Nijeriya, da kuma yin furofaganda kan al'adun kasar Sin da kamfanin, tun daga watan Mayu a shekarar 2008, kamfanin ya fara yin hadin gwiwa tare da wata kungiya ta kasar Nijeriya da ba ta gwamnatin ba, sun zabi 'yan makaranta 25 masu fama da talauci daga makarantu guda 5 da su shiga wani kwas din horaswa wajen koyon Sinanci a kyauta.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan watanni uku da rabi, yara na wannan kwas din koyon Sinanci sun riga sun gama aikinsu. Ruth wata Yarinya mai koyon Sinanci mafi kyau za ta sami tikitin jirgin sama da kamfanin ya bayar, kuma a watan Agusta, za ta je birnin Beijing, babban birni na kasar Sin don kallon gasar wasannin Olympics.(Abubakar)