Ran 3 ga watan Yuli, yayin da mataimakin ministan tsaron zaman lafiya na kasar Sin Meng Hongwei ya halarci taro na karo na 12 na kwamitin hukumar kula da yaki da ta'addaci na kungiyar hada kan birnin Shanghai, ya bayyana cewa, kungiyoyin tsaro na gasar wasannin Olympic ta Beijing sun riga sun gudanar da hakikanin matakai, kasar Sin tana da kwarin gwiwa wajen ba da tabbaci ga shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing lami lafiya.
Meng Hongwei ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin tana da zaman lafiya da lumana a gida haka kuma ta sami sakamako mai kyau wajen siyasa da tattalin arziki da al'adu, wannan ya aza harsashi mai kyau ga shirya gasar wasannin Olympic lami lafiya.
Meng Hongwei ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, sassan da abin ya shafa wajen kula da harkokin tsaro na kasar Sin sun riga sun dauki hakikanan matakai, don magance kalubalen da Sin za ta iya fuskanta a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing. A sa'i daya kuma, ayyukan ba da tabbaci ga tsaron gasar wasannin Olympic ya sami goyon baya daga bangarorin daban daban na kasashen duniya, wadannan matakan da aka dauka sun karfafa zukatan mutanen kasar Sin wajen ba da tabbaci ga shirya gasar wasannin Olympic lami lafiya.(Bako)
|