
A ran 4 ga wata da safe da misalin karfe 8, an fara mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Xi'an na lardin Shanxi.

Tian Liang zakaran wasan yin tsalle cikin ruwa na wasannin Olympic ya dauki wutar yola ta farko da aka mika a birnin Xi'an, kuma ya fara mika wutar daga filin hasumiya mai suna Xiaoyan na birnin Xi'an. Wurin karshe da za a kai wutar shi ne filin hasumiya mai suna Ziyun. Dukan tsawon hanyar da ake bi wajen mika wutar ya kai kilomita 9.2, Yawan jama'ar da suka dauki wutar yola ya kai 208, za a mika wutar fiye da awoyi 2.(Abubakar)
|