Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-04 15:31:41    
Sinawa dake zaune a hedkwatar wasannin Olympics suna goyon bayan gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, birnin Lausanne dake yammacin kasar Swiss, babban zaure na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC, kuma wuri ne dake kasancewar dakin nune-nune na wasannin Olympics na duniya. Saboda haka ne, mutane ke kiransa " Hedkwatar Wasannin Olympics". Kwanan baya ba da dadewa ba, Sinawa da kuma Sinawa 'yan kaka-gida sama da 800 daga wurare daban-daban na kasar Swiss har da wassu aminai na kasar Sin sun taru a nan don nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing yayin da suke karfafa aniyar kasar Sin. ' Ana yin wannan kirari ne da babbar murya. Hadaddiyar kungiyar sada zumunta tsakanin kasashen Swiss da Sin ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan harka yayin da take samun amincewa da gwamnatin jihar Vaud, inda 'yan sanda suka kare oda a wurin. A wancan rana da yamma da misalin karfe biyu,Sinawa da Sinawa 'yan kaka-gida, da dalibai da kuma ma'aikata na kasar Sin da suke aiki a hukumomin kasa da kasa su kimanin dari shida zuwa dari bakwai, wadanda suka zo daga biranen Lausanne, da Geneva, da Zurich, da Basel, da kuma Fribourg da dai sauransu na kasar Swiss sun taru a wani karamin fili dake waje da dakin nune-nune na wasannin Olympics na duniya rike da tutocin mulkin kasar Sin, da tutocin kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, da tutocin gasar wasannin Olympics ta Beijing, da kuma tutocin mulkin kasar Swiss; kuma suna sanye da rigunan T-shirt da suka rubutun kalmomin " Ina kaunar kasar Sin" cikin Turanci a kai; Sa'annan sun tsaya cik domin nuna babban alhininsu ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon babbar girzigar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Daga baya, sun yi maci zuwa babban zauren kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa dake da tazarar kilo-mita 3.5 daga wurin, inda suka yi ta yin sowwa cikin Sinanci, da Fransanci da kuma Turanci a kan cewa: " Sa kaimi, kasar Sin"! " Sa kaimi, kasar Sin"! " Muan marhabin da ku don ku je Beijing !''

Dukkanin mahalarta taron sun zo bakin kofar ginin babban zauren kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, inda mai shirya taron ya karanta wani sako a fili zuwa ga shugaba Jacques Rogge na kwamitin domin nuna goyon gaya da kauna ga gasar wasannin Olympics ta Beijing.

" A nan, babban zauren wasannin Olympics, muna so mu fadi cewa muna goyon bayan gasar wasannin Olympics ta Beijing. Daidai kamar yadda kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya bayyana ne, gasar wasannin Olympics, wata gagarumar gasa ce ta wasannin motsa jiki. Bai kamata a sanya siyasa a cikinta ba. Dukkanmu muna ganin cewa, gasar wasannin Olympics, wata gasa ce mai kayatarwa, wadda mutane masu bambancin al'adu da addinai suke karawa tsakaninsu bisa matsayin daidaici domin kara inganta zumunci".

Ko kuna sane da cewa, jihar Vaud ta Swiss, wata jiya ce dake yin kawanya da lardin Shanxi na kasar Sin. Shugaban hadaddiyar kungiyar sada zumunta tsakanin jihar Vaud da lardin Shanxi Mr. Rene Pfiffer shi ma ya halarci taron, inda ya furta cewa: " Kasar Sin za ta gudanar da gasar wasannin Olympics nan ba da dadewa ba. Mu kam muna farin ciki matuka kamar yadda jama'ar kasar Sin suke . Kasar Sin kasa ce mai girma wadda take da dadadden tarihi na tsawon shekaru dubu biyar. Ina cike da imanin cewa, za a cimma nasarar gudanar da wannan gagarumar gasa. A lokaci guda, ina bakin ciki matuka saboda rasuwar mutane da yawa a sanadiyyar bala'in girgizar kasa mafi muni da ya auku a lardin Sichuan na kaksar Sin".

Game da gasar wasannin Olympics ta Beijing da za a gudanar, Sinawa masu yawan gaske dake zaune a kasar Swiss sun nuna kyakkyawan fatan alheri. Madam Mo Shuping, wakiliyar Sinawa daga bangaren kasuwanci ta fadi cewa: "Dukkaninmu kakanin-kakanin al'ummar kasar Sin ne. Kowa da kowa na da alhakin bauta wa kasar mahaifa. Tuni a shekarar 2001 lokacin da kasar Sin ta samu iznin shirya gasar wasannin Olympics, ko wane dan iyalin mahaifarmu na sa ran gudanar da wannan gagarumar gasa tare da nasara. A 'yan shekarun baya, mun gane ma idonmu babban ci gaban da kasar mahaifarmu ta samu; kuma duk duniya ita ma ta ga wata kasa mai tohon wadata".

Kafin a kawo karshen taron, dukkan mutane sun rubuta sunayensu kan wata tuta mai zobba biyar don bayyana kyakkyan fatansu ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. ( Sani Wang )