Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-04 15:28:11    
Waiwaye Adon tafiya(9)

cri

Lubabatu:Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a filinmu na amsoshin wasikunku, inda yau za mu ci gaba da gabatar muku shirinmu na "waiwaye adon tafiya", wato shirin musamman na murnar cika shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, a cikin shekaru 45 da suka wuce, sashen Hausa ya kulla zumunta da masu sauraronsa da yawa. A kasar Nijer ma, ba mu rasa aminai masu sauraronmu ba. Musamman bayan da sashen Hausa ya fara kaddamar da shirye-shiryensa a birnin Yamai ta zangon FM 104.5 tun daga ran 10 ga watan Afril na shekarar 2006 da kuma shirye-shirye na tsawon awa shida da ya soma watsawa ta zangon FM 106 daga watan Oktoba na shekarar 2007 da ta gabata, masu sauraronmu a birnin Yamai sai kara karuwa suke yi, wadanda suke nuna himma wajen sauraron shirye-shiryen sashen Hausa na rediyon kasar Sin, har ma sun kafa wata kungiyar masu sauraron gidan rediyon kasar Sin, wadda ke da sunan "Nesa ta zo kusa". To, masu sauraro, kwanan baya, ta wayar tarho ne, wakilinmu a Lagos, Bello ya sami damar yin hira da shugaban wannan kungiya, wato malam Mamane Ada, to, a cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku labarin masu sauraronmu a birnin Yamai.

Bello:Malam Mamane, da farko, ko za ka gabatar da kanka zuwa ga masu sauraronmu?

Mamane: Sunana Mamane Ada, kuma ina aiki a nan gidan rediyon R&M, da ke birnin Yamai, a jamhuriyar Nijer.

Bello:A matsayinka na shugaban kungiyar masu sauraro ta Nesa Ta Zo Kusa, don Allah, ka yi bayani a kan kungiyar.

Mamane:E, to, na gode, malam Bello, da ka ba ni damar in ba da ra'ayina a kan wannan kungiya tamu da ke nan birnin Yamai, wadda masu sauraro watakila suka ji an bayyana sunanta cewa, "nesa ta zo kusa". To, a gaskiya, dalilin kafa wannan club na "nesa ta zo kusa" yana da tarihi mai kyau, domin tun fil azal dai, mu muna sha'awar sauraron gidan rediyon kasar Sin, sai ga shi Allah ya sa gidan rediyon kasar Sin ya zo nan birnin Yamai, inda yake watsa shirye-shiryensa a kan FM, wato gajeren zango 106, kuma yana watsa shirye-shiryensa a nan tashar gidan rediyon R&M, a gajeren zangon FM na 104.5, wannan ya sa na yi nazari na ce, to, me ya kamata mu yi, don kara cigaban wannan gidan rediyon kasar Sin. Sai na ga ya kamata mu shirya mu kawo kungiya, wadda muka sa ta sunan "nesa ta zo kusa", ma'ana dukan mutanen da ke da ra'ayin gidan rediyon kasar Sin da kuma masu sauraron gidan rediyon Sin, sai munka yi shawara tsakaninmu, muka kawo wannan kungiya mai suna "nesa ta zo kusa". Me ya sa muka ce "nesa ta zo kusa", sabo da mu muna nan nahiyar Afirka, musamman ma muna nan a jamhuriyar Nijer, kuma daga inda kasar Sin take, tana da nisa kwarai da kasarmu ta Nijer, ke nan abin da sai mun saurare shi ta tashar daji, ga shi yanzu ya zo kusa da mu, wannan shi ne ya sa muka sa wannan kungiya tamu nesa ta zo kusa. Kuma a yanzu, kungiya tamu tana da kusan wata shida da kafawa, kuma mun kafa ta ne, a tsakani akwai maza akwai mata, akwai ma'aikata na gwamnati, akwai 'yan kasuwa, akwai ma'aikatan gidan rediyo, kuma muna ba da hankali a game da makomar da ita rediyon ainihin kasar Sin take sa gaba, shi ne kara huldar zumunci a tsakanin kasashen duniya, musamman ma kasashen nahiyar Afirka da Sinawa a doron duniya.

Bello:Yaya jama'ar Yamai ke karbar wannan gidan na FM106? Suna sauraron FM din ba? Suna son shirye-shiryen da ake watsawa ba?

Mamane:Malam Bello, ina fatan Allah ya kawo ka nan birnin Yamai, da kai da kanka za ka tabbatar da cewa, gaskiya, mutanen Yamai suna sauraron wannan tasha ta CRI, saboda idan ka yi yawo cikin birnin Yamai, in ka shiga gidaje cikin birnin Yamai, za ka ji ko kan hanya ne za ka ji wasu kide-kide na kasar Sin, ko kuma wasu shirye-shirye mutane suna saurare, wato ke nan, ana iya cewa, an karbi wadannan shirye-shirye na gidan rediyon kasar Sin da hannu biyu biyu. Wato in an misalta shi, ana iya cewa, kashi 60% na mutane suna sauraron CRI a nan Yamai da kuma kewayenta.

Bello:A cikin shirye-shiryenmu daban daban, wane ne masu sauraronmu suka fi so?

Mamane: Masu sauraro a nan Yamai, akasari suna sauraron labaru, suna ba da hankali a kan labaru. Sa'an nan, da wannan fili na Halima da Balarabe Shehu Ilelah, wato "koyon Sinanci", sa'an nan "me ka sani game da kasar Sin" shi ma mutane suna saurare, kuma "amsoshin wasikunku", shi ma mutane suna saurare, kuma "musulunci a kasar Sin", shi ma ana saurare, ka ga zan ce malam Bello, dukannin shirye-shiryen da gidan rediyon kasar Sin ke yi ta wannan gajeren zango na 106 a nan birnin Yamai, mutane suna saurare a ko da yaushe, kuma a ko da yaushe mutane suna cewa, "muna son shiga wannan kungiya taku, muna son shiga wannan kungiya taku."

Bello:A ganinka, ina bambancin da ke tsakanin CRI da sauran kasashen yamma?

Mamane:Akwai bambanci kwarai da gaske. ka ga wajen aikin jaridanci ma anka yi amfani da yadda dokokin aikin jarida ya bayyana da kuma a ce a yi amfani da dokokin aikin jarida ta rubutawa ce ko kuma ta radio ce to, In ka kimanta yadda CRI take nasa aiki, za ka gane cewa, akwai bambanci kwarai da gaske. Me ya sa na ce akwai bambanci, sabo da akasarin rediyo, kamar muryar Amurka ko BBC ko R5, za ka ga lalle, in suna ba da wasu shirye-shiryensu, ko kuma suna kaddamar da labaransu, sai ka yi tsammanin akwai wani abu na son kai a ciki. Ita rediyon kasar Sin, shirye-shiryenta, dukanninsu ake iya amfani da su. Ko ba dan kasar Sin ba ne, in ka saurari shirye-shiryen gidan rediyon Sin, za ka ga wannan gidan rediyo yake aiki domin cigaban al'ummar kasashen duniya, domin kara dankon zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da ma duniya baki daya, ke nan nake cewa, ma'aiktan CRI suna aiki kamar yadda dokokin jarida suka ce, kuma mutane suna karuwa da shirye-shiryensu, mutane suna ba da ra'ayoyinsu, kuma suna aiki da wannan shawarar da suke ba da, domin kome ya zo daidai da aikin wannan gidan rediyo.

Lubabatu:To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, amma kada ku manta, a makon gobe war haka, za mu ci gaba da kawo muku shirye-shiryenmu na "waiwaye adon tafiya", da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, "sai Allah ya kai mu ranar Jumma'a mai zuwa. (Lubabatu)