|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-07-03 19:39:33
|
An samu nasarar yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a biranen Yangling, da Xianyang
cri
Yau 3 ga wata, an samu nasarar yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a biranen Yangling, da Xianyang na lardin Shanxi na kasar Sin.
Birnin Yangling birni ne da fasahar aikin gona na kasar Sin ta samo asali. Yau da safe da karfe 8, an soma bikin yawo da fitilar a birnin, masu yawo da fitilar da yawansu ya kai 95 sun halarci bikin, a yau da tsakiyar rana an kawo karshen bikin a birnin Yanglin.
Bayan haka kuma, a wannan rana da yamma, an soma yawo da fitilar wasannin Olympics a birnin Xianyang, wato zango na biyu da aka yi bikin a yau. Masu yawo da fitilar 113 sun halarci bikin.
A ranar 4 ga wata kuma, za a cigaba da bikin yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Xi'an, hedkwatar lardin Shanxi. (Bilkisu)
|
|
|