Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Liu Jianchao ya bayyana yau 3 ga wata a nan birnin Beijing cewar, ko-ta-kaka bangaren Sin ba zai amince da a saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics ba. Ya ce, duk wani yunkurin saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics, da yin shiga-sharo-ba-shanu cikin harkokin gidan kasar Sin zai ci tura!
A wajen taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya a wannan rana, wani dan jarida ya yi tambaya cewa, akwai kasashe kalilan wadanda suka saka batun siyasa a cikin gasar wasannin Olympics. To, menene ra'ayin bangaren Sin dangane da wannan lamari?
Liu Jianchao ya amsa cewar, bisa ra'ayin "Tsarin Mulkin Olympics", bai kamata ba a saka batun siyasa cikin gasar wasannin Olympics, ya kamata daukacin kasashe membobin gasar wasannin Olympics su mutunta wannan ra'ayi. Ko-ta-yaya bangaren Sin ba zai amince da a saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics ba!(Murtala)
|