Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-03 17:01:08    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Malaman koyarwa sun nuna bajinta wajen yaki da 'yan banga.An sami wasu malaman koyarwa wanda shugaban makaranta shi ne jagora sun murkushe wani harin da wasu 'yan banga suka kai wa makaranta a birnin Siping na lardin Jilin dake arewa maso gabacin kasar Sin. Da 'yan banga suka shiga makaranta da hari,shugaban makaranta mai suna Dong ya kama gaba,dauke da kanana duwatsu a hannu,tare da wasu malaman koyarwa maza sun tsaya gaban kofofin dakunan koyarwa domin kare 'yan makaranta daga harin 'yan banga,malaman koyarwa mata sun sun kirawo 'yan sanda. Da ya ke wani malamin koyarwa ya ji rauni maras tsanani a cikin fada, yan banga sun dakatar da kai hari sun gudu sa'ad da 'yan sanda suka isa wurin.yanzu 'yan sanda suna farautar wadannan 'yan banga matasa.

Mutane masu tarin yawa sun ba da taimakon jini bayan da gidan rediyo ya watsa labari. Mazauna sama da dari biyar na birnin Changchun,babban birnin lardin Jilin dake arewa maso gabachin kasar Sin sun hallara a asibitin dake cibiyar birnin domin ba da taimakon jini ga wata mata mai ciki da take bukatar jini mai nau'in B. babu abin da za a yi sai aka kai mata mai ciki daga wani asibiti zuwa wani daban a birnin Changchun domin a yi mata fida da cire da a ranar lahadi domin jini ya yi karanci.likita ya ce ran matar na hannun Allah idan an gaza samun jinin da ake bukata. Bayan da gidan rediyon birnin ya watsa labarin nan,sai nan da nan mazauna fiye da dari biyar sun hanzarta zuwa asibitin da matar ta kwanta a ciki, sun bayar da taimakon jini. Daga bisani matar ta haifar da da lami lafiya,iyalan matar ya gode wa wadanda suka bayar da taimakon jini da asibitin da kuma gidan rediyo bisa kokarin da suka yi.

Wani da ya shirya bikin jana'iza domin mamarsa. A ran 13 ga watan Maris na shekarar bara,wata karamar mota da Hu Chunguang ya tuka ta bugi mamarsa har lahira yayin da take kokarin tura motar da ta nuntse cikin dusar kankara.dan ya yi bakin ciki kwarai da gaske yana so ya yi diyya ga uwarsa da shirya mata kasaitacciyar jana'iza.yana so ya yi amfani da kudin ta hanyar inshora.amma kamfanin inshora ya ki ya biya masa kudin domin ya yi inshora ne tsakaninsa da kamfani kawai,inshora ba ya shafi wani bangare daban.

Wani mai kwashe shara ya samu kudin Bonus saboda ya mayar da fartamami ga mai shi.An sami wani tsohon mai kwashe shara dake da yawan shekaru 62 da haihuwa a birnin Bazhou na lardin Hebei dake arewancin kasar Sin da ya samu kudin Bonus bayan da ya tarar da fartamami dake kunshe da kudade da kati da yawansu ya kai kudin Sin Yuan sama da miliyan daya ya kuma mayar da shi ga mai shi. Mr Sun Chengzhe ya gano fartamami ne a wani bayangida dake gefen hanya yayin da ya kwashe shara a wurin a ran daya ga watan Fabrairu. Da ya bude fartamami ya tsabar kudi dubu biyu da dari bakwai da kuma katin kudi biyar da sauran muhimman takardu,ciki har da takardar shaida matsayinsa wato ID card da takardu game da lafiyarsa. Da ya ke bai taba ganin yawan kudin kamar hakan a duk rayuwarsa, ya mika duk takardun ga kwamitin kula da kauye,kwamitin ya yi cudanya da mutumin da ya rasa abinsa.daga bisani mai rasa abin ya zo ya tara abinsa ya kuma gode wa mr Sun Chengzhe.