Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 21:36:50    
Wen Jiabao ya ce, har kullum gwamnatin kasar Sin tana tsayawa kan mayar da babbar moriyar jama'a a gaban kome da bude kofa ga duniya a yayin da take yaki da girgizar kasa

cri

A yayin da yake ganawa da baki daga kasar Amurka a ran 2 ga wata a birnin Beijing, firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya ce, har kullum gwamnatin kasar Sin tana tsayawa kan mayar da babbar moriyar jama'a a gaban kome da bude kofa ga duniya a yayin da take yaki da girgizar kasa, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin da take iya yi domin tabbatar da zaman lafiyar jama'a, da kuma tsugunar da su yadda ya kamata, da yin amfani da duk karfin kasar Sin wajen taimakawa jama'ar yankunan girgizar kasa kan sake gina gidajensu.

A ran nan, Mr. Wen ya gaba da hadaddiyar tawagar wakilai ta gwamnatin kasar Amurka da kamfanoni da kungiyoyin ba da agaji na kasar Amurka, wadda darektan hukumar raya kasa da kasa ta Amurka Mr. Henrietta Fore da shugaban kamfanin Johnson Mr. Bill Weldon suka shugabanta.

Mr. Wen ya yi maraba da tawagar wakilai ta kasar Amurka ta yi rangadi a yankunan girgizar kasa, domin nazarin yadda za ta halarci aikin sake gina gidaje bayan girgizar kasa.

Mr. Fore ya ce, kasar Amurka tana son hada kai da kasar Sin, tana son yin kokari bisa karfinta domin taimakawa jama'ar yankunan girgizar kasa, da kuma kara sada zumunda da hadin kai da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu.(Danladi)