Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 17:41:09    
Kasar Sin za ta yi amfani da fasahar da kasar Japan ta samu wajen farfado da wuraren da ke fama da bala'in girgizar kasa

cri
Ana nan ana yin taron hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan yau a nan birnin Beijing don tattauna batun farfado da wuraren da mummunan bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a lardin Sichuan na kasar Sin. A gun taron mahukuntan kasar Sin da na Japan sun bayyana cewa. Cikin yunkurin farfado da wuraren da ke fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, kasar Sin za ta yi amfani da sakamakon da kasar Japan ta samu daga wannan fanni. An ce, a nan gaba kasar Japan za ta aika da kwararrunta da abin ya shafa zuwa lardin Sichuan don taimakawa da kuma ba da jagara ga ayyukan farfado da wadannan wurare.

A ran 1 ga wata a nan birnin Beijing, an bude taron kara wa juna ilmi tsakanin Sin da Japan domin farfado da wuraren da mummunan bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a lardin Sichuan na kasar Sin, da akwai goman jami'ai da kwararru wadanda suka zo daga kasar Sin da Japan sun halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu.

Mr. Li Youxian, mataimakin shugaban hukumar gine-gine ta lardin Sichuan wanda ya halarci taron ya bayyana cewa, "Bayan aukuwar wannan mummunar girgizar kasa a lardin Sichuan, gwamnatin Japan ta mai da hankali sosai kan babbar hasarar da aka samu sakamakon bala'in, jama'ar da ke wurare masu fama da bala'in suna nuna godiya ga kasashe daban-daban ciki har da Japan bisa taimakon da suka ba mu. Kasar Japan takan gamu da girgizar kasa, sakamako ko darussa da ta samu daga wasu fannoni su ma suna da amfani gare mu, muna fatan za mu yi amfani da su bisa matsayin fasaha."

Mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 8 da ta faru a ran 12 ga watan Mayu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu 69, fadin wuraren da girgizar kasar ta ritsa da su ya wuce murabba'in kilomita dubu 100.

Mr. Koga Shigenari, shugaban ofishin kula da harkokin kasar Sin na hukumar hadin gwiwa tsakanin Japan da sauran kasashen duniya ya bayyana cewa, "Za mu yi wa kasar Sin bayani kan sakamako da darassu da Japan ta samu daga wannan fanni. Ta hanyar taron kara wa juna ilmi da ake yi a yau, za mu iya fahimtar abubuwan da wurare masu fama da bala'in suke bukata, wannan yana da amfani ga yin ayyukan hadin gwiwa wajen fasaha, ciki har da aika da kwararrun Japan zuwa lardin Sichuan."

Mr. Koga Shigenari ya bayyana cewa, yanzu hukumar hadin gwiwa tsakanin Japan da sauran kasashen duniya tana gudanar da wasu ayyukan hadin gwiwa a lardin Sichuan na kasar Sin, ciki har da farfado da tsire-tsire da aka lalata sabo da girgizar kasa, da yin rigakafin annoba a wurare masu fama da bala'in, da kuma warka da wadanda suka ji rauni mai tsanani.

Sa'an nan kuma Mr. Koga Shigenayi ya bayyana cewa, "Ayyukan da gwamnatin kasar Sin ta yi domin tinkarar bala'in girgizar kasa a wannan gami, sun ba mutanen Japan mamaki kwarai. Da farko, ta aika da mutane masu aikin jiyya da kungiyoyi masu yin ceto zuwa wurare masu fama da bala'in da saurin gaske. Na 2, ta tayar da mutanen duk kasar Sin don su ba da taimako ga masu jin rauni sabo da girgizar kasar." (Umaru)