Mai sauraronmu zakaran gasar ilmin wasannin Olympic na gidan rediyon kasar Sin ya ziyarci cibiyar jirgin ruwa mai filafili ta birnin Qingdao dake bakin teku na gabashin kasar Sin a ran 2 ga wata, kuma ya nuna babban yabo ga wannan cibiyar.
Tun daga watan Mayu zuwa watan Nuwamba na shekarar bara, gidan rediyon kasar Sin ya yi gasar ilmin wasannin Olympic a duk duniya, kuma mun samu takardun amsa dubu 720 daga kasashe da yankuna fiye da 140. Sa'an nan, mun zabi zakaru 8 daga cikinsu don kawo wa kasar Sin ziyara daga ran 26 ga watan da ya wuce zuwa ran 3 ga wannan wata. Wadannan zakaru sun fito daga kasashen Amurka da Jamus da Tanzania da kuma sauransu.(Lami)
|