Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 15:32:13    
Kai ziyara ta musamman ga 'yar wasan harba kibiya ta farko ta kasar Sin a gun gasar wasannin Olympics

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an gudanar da gasar cin kofin Larabawa ta wasan harba kibiya a shekarar 2008 kwanakin baya ba da jimawa ba a kasar Qatar. A wurin gasa dake karkarar birnin Doha, hedkwatar kasar Qatar, wakilinmu ya samo Madam Li Lingjuan, babbar mai koyar da 'yan wasan harba kibiya na kasar Qatar. In ba a manta ba tuni yau da shekaru 24 da suka gabata, Madam Li ta wakilci kasar Sin ga shiga gasar wasannin Olympics ta 23 ta Las Angeles a kasar Amurka. Kuma yau da shekaru 6 da suka shige, kwamitin wasan motsa jiki na kasar Sin ya tura ta zuwa kasar Qatar wajen kafa kungiyar wasan harba kibiya ta mata ta kasar. A gun gasar wasannin motsa jiki na Asiya da aka gudanar, madam Li ta ja ragamar kungiyar wasan harba kibiya ta mata ta kasar Qatar ga karya matsayin rashin samun lambar yabo ko daya da kasar din ta samu a gun gasannin da aka gudanar a da. Saboda haka ne dai, 'yan kasar Qatar suke kiranta " Jarumar al'umma".

A lokacin da Madam Li Lingjuan take waiwayen tarihinta na shiga gasar wasannin Olympics a karo na farko a madadin kasar Sin yau da shekaru 24 da suka gabata, ta furta cewa: " Shekaru biyu da rabi kawai da ta soma samun horon wasan harba kibiya kafin ta shiga gasar wasannin Olympics ; kuma a wancan lokacin, ita wata yarinya ce mai shekaru goma sha takwas da haihuwa, wadda ba ta san shin mene ne wasannin Olympics ba, sai kawai ta san cewa gasar wasannin Olympics wata gasar wasanni ce mafi kayatarwa a duk duniya. Lallai bikin bude gasar wasannin ya sosa zuciyata kwarai da gaske. Na yi alfahari shiga irin wannan gagarumar gasa da kasashe 178 suka halarta .''

Madam Li Lingjuan ta ci gaba da cewa, a gun gasar wasannin Olympics ta Las Angeles a shekarar 1984, kungiyar wasan harba kibiya ta kasar Sin da ta shiga gasar wasannin Olympics a karo na farko ta kara da kungiya kakkarfa ta Korea ta Kudu. Ko da yake Madam Li ta karya matsayin bajimta na wasannin Olympics a fannin ayyukan wasa guda biyar, amma duk da haka, lambar azurfa ce kawai ta samu. Lallai ta nuna bacin rai. Kawo yanzu dai, kasar Sin ta rigaya ta samu lambobin azurfa guda biyar a fannin wannan wasa, amma abin bakin ciki shi ne ko lambar zinariya daya ba ta samu ba tukuna. Madam Li ta furta cewa : " Ba zan manta da halartar gasar wasannin Olympics da na yi a karo na farko a duk tsawon raina ba. Ko da yake na zo ta biyu wajen samun lambobin yabo a gun wasannin harba kibiya, amma kungiyar kasarmu ta sha kaye yayin da take karawa da kungiyar Korea ta Kudu. Cikin shekaru sama da ashirin da suka gabata, har kullum kungiyar korea ta Kudu tana kan gaba a fannin irin wannan wasa. Ina fatan 'yan wasa na kasar Sin za su lashe na Korea ta Kudu a gun wasannin Olympics na Beijing". Madam Li Lingjuan ta ci gaba da cewa, shiga wasannin Olympics da samun lambar zinariya, kyakkyawan buri ne na wani dan wasa; kuma wata kasa da ta samu damar gudanar da gasar wasannin Olympoics, lallai abu ne da ya cancanci a yi alfahari a kai. Akwai mutane kalilan da suke yunkurin kaurace wa gasar wasannin Olympics ta Beijing, wannan dai na alamanta cewa ba sa son ganin wata sabuwar kasar Sin. Madam Li Lingjuan ta kuma jaddada cewa, wa'adin wasannin motsa jiki na wani dan wasa kimanin shekaru goma ne kawai. Mene ne hasashen wasannin Olympics? Ai ma'anar hasashen ita ce, jama'ar duniya baki daya su hadu gu daya a albarkacin wannan gagarumin biki ba tare da nuna bambancin asalin kasashe da kuma launin fata ba. Dadin dadawa, Madam Li Lingjuan ta furta cewa: " A ganina, hasashen wasannin Olympics, hasashe ne shiga wasannin. Kamata ya yi a ba wa kowane dan wasa damar shiga wasannin. Bai kamata ba wassu shugabannin kasashen duniyar yamma su haramta halallen ikon 'yan wasansu na shiga gasar wasannin Olympics."

A karshe dai, Madam Li Lingjuan ta yi imanin cewa, kasar Sin za ta iya gudanar da wata gagarumar gasar wasannin Olympics tare da samun nasara mafi girma. Kuma ta ce, wannan ma sahihiyar zuciya ce da aminai baki masu tarin yawa da take aiki tare da su suke nuna wa jama'ar kasar Sin.( Sani Wang )