Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-01 22:03:38    
Ana mayar da al'amuran aikin kawo albarka, da zaman rayuwa su koma yadda ya kamata a yankuna masu fama da bala'i na lardin Sichuan

cri

Yau 1 ga wata a birnin Chengdu, mataimakin shugaban lardin Sichuan Mr. Huang Xiaoxiang ya bayyana cewa, yanzu ana mayar da al'amuran aikin kawo albarka, da zaman rayuwa su koma yadda ya kamata a yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan.

Mr. Huang Xiaoxiang ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake yin shawarwari tare da wakilai daga hukumar raya kasa ta duniya ta kasar Amurka, da masana'antun kasar, da kuma kungiyoyin da ba na gwamnati ba. Mr. Huang ya bayyana cewa, a sakamakon wannan babbar girgizar kasa da aka samu a Wenchuan, ba wanda ya mutu saboda yunwa, kuma ba a samu bullar annobar ba, bayan haka kuma, babu wanda ya mutu a sanadiyar bala'un da girgizar kasar ta haddasa.

Har wa yau kuma, bisa kididdigar da aka yi an ce, ya zuwa ranar 1 ga wata da karfe 12, mutane 69,195 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da aka samu a dunguar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da mutane fiye da 370,000 suka ji rauni, kuma wadanda sama da 18,000 suka bace.

Kazalika kuma, ya zuwa ranar 1 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyaki da darajarsu ta kai kusan kudin Sin RMB yuan biliyan 55.4 daga bangarori daban daban na gida da waje. (Bilkisu)