Ran 30 ga watan Yuni a nan birnin Beijing, an bayar da tashoshin mutane masu aikin sa kai na wasannin Olympics na Beijing, kuma masu aikin sa kai sun far aiki a yau ran 1 wannan wata.
Tun daga ran 1 ga watan Yuli, bi da bi ne masu aikin sa kai dubu 400 za su fara aiki a tashoshi 500 a birnin Beijing, za su samar da aikin hidima ga membobi na babban iyalan wasannin Olympics, da manema labaru na gida da na waje, da 'yan kallo, da masu yawon shakatawa da kuma mazaunan birnin Beijing kan fannonin amsa tambayoyi, da tinkarar matsaloli cikin gaggawa, da kuma aikin fassara.
Musu aikin sa kai na wasannin Olympics na Beijing za su samar da aikin hidima tun daga ran 1 ga watan Yuli zuwa ran 8 ga watan Oktoba, tsawon wa'adin aikinsu ya kai kwanaki 100. Tsawon lokacin ayyukansu ya kai awoyi 8 a ko wace rana, kuma za su yi aikin hidima a awoyi 24 a ko wace rana a kwanaki na musamman.
|