Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-01 10:55:59    
Gwamnatin kasar Sin ta bayar da manufofin goyon baya ga ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa

cri

A ran 30 ga wata, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da "ra'yoyi game da manufofin nuna goyon baya ga ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na Wenchuan". Wannan takarda ta shafi fannoni daban daban kan yadda za a farfado da ayyukan kawo albarka da sake raya yankuna masu fama da bala'in, an kuma bayar da dimbin hakikanan manufofin nuna goyon bayansu da za a iya aiwatar da su cikin sauki.

A cikin wannan takarda, a fili ne aka nuna cewa, za a kebe kudade daga baitulmali na tsakiya domin kafa asusun sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa, kuma za a dauki matakan samar da tallafin kudi ga mazauna da ayyukan zuba jari da kuma samar da rancen kudin da gwamnatin za ta ba da tallafin kudin ruwa domin nuna goyon bayan ayyukan sake gina gidajen da mazauna birane da na kauyuka za su yi da farfado da ayyukan jama'a da na yau da kullum da farfado da aikin gona da na masana'antu. A waje daya kuma, an bayyana cewa, gwamnati ce za ta kara mai da hankali kan samar da ayyukan jama'a da na yau da kullum da suke moriyar jama'a. Bugu da kari kuma, za a bi hanyar kasuwanci lokacin da ake farfado da masana'antu da kasuwanni. Masana'antu su da kansu ne za su farfado da aikinsu, kuma gwamnati za ta nuna musu goyon baya a fannin haraji da kasafin kudi, sabo da haka, bankuna za su iya samar musu rancen kudi cikin yakini.

Haka kuma, an tsai da hakikanan kuduran nuna goyon baya ga kokarin samar da guraban aikin yi da kuma samar da tallafi kudi ga inshorar ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a. (Sanusi Chen)