Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 21:04:51    
Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yi godiya ga kasashen duniya da su nuna goyon baya kan aikin yaki da bala'in girgizar kasa na Sin

cri
A ranar 30 ga watan Yuni, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da wata sanarwa, inda ta yi godiya ga kasashen duniya da suka nuna goyon baya, da bayar da taimako kan aikin yaki da bala'ain girgizar kasa da ceto mutane na kasar Sin.
|
Sanarwar ta nuna cewa, babbar girgizar kasa mai karfin digiri 8 da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, ta haddasa babbar hasarar rayuwa da ta dukiyoyi. A lokacin da jama'ar kasar Sin ke shan wahala sosai a sakamakon wannan babban bala'i, kasashen duniya sun nuna tausayi da gaisuwa da zuciya daya, a waje daya kuma sun nuna goyon baya, da bayar da taimako ta hanyoyi daban daban ga kasar Sin. Gwamnati, da jama'ar kasar Sin sun yi godiya sosai ga gwamnatocin kasashe, da kungiyoyin kasashen duniya, da 'ya'yan Sinawa mazaunen kasashen ketare, wadanda suna nuna tausayi sosai, da bayar da muhimman taimako ga kasar Sin.

Bugu da kari kuma, sanarwar ta bayyana cewa, bayan faruwar bala'in, kasar Sin ta yi iyakacin kokari, don yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane, har ma ta samu nasara sosai bisa mataki. (Bilkisu)