Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 21:03:32    
An kammala aikin bada tabbaci ga sufuri na gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
Zuwa yau ranar 30 ga watan Yuni, an riga an kammala aikin bada tabbaci ga sufuri da zirga-zirga ta gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Mai magana da yawun ma'aikatar kula da harkokin zirga-zirga da sufuri ta kasar Sin He Jianzhong ya bayyana cewar, yanzu an riga an kammala aikin bada tabbaci ga zirga-zirgar hanyoyin mota dake shafar gasannin Olympics, da aikin bada tabbaci da hidima ga bikin zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics, da aikin kafa kungiyar motoci domin biyan bukatun gaugawa, da aikin kyautata ingancin iskar da motocin da suka shiga cikin birnin Beijing suka fitar da dai sauran makamantansu.

He Jianzhong ya yi nuni da cewar, ma'aikatar kula da harkokin zirga-zirga da sufuri ta kasar Sin ta kafa "hanyar da za'a bi cikin gaugawa domin gasar wasannin Olympics" a nan kasar Sin, ta yadda za'a bada tabbaci ga zirga-zirgar motoci wadanda ke da lasisi na musamman na gasar wasannin Olympics ba tare da shamaki ba. Hakazalika kuma, mutanen da za su gudanar da harkokin gasar wasannin Olympics ta Beijing sun riga sun shirya sosai a kan harsunan waje.(Murtala)