Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 16:00:53    
Mugabe ya sami nasarar babban zaben shugaban Zimbabwe

cri
Ran 29 ga wata, kwamitin zabe na kasar Zimbabwe ya sanar da cewa, shugaba mai ci yanzu kuma dan takarar jam'iyyar ZANU-PF da ke mulkin Zimbabwe Mr. Robert Mugabe ya sami nasarar kada kuri'a a zagaye na 2 na babban zaben shugaban kasar. Daga baya, Mr. Mugabe ya yi bikin rantsuwar kama aiki, inda ya bayyana cewa, yana son yin shawarwari da jam'iyyun 'yan hamayya. Sa'an nan kuma, zai halarci taron shugabannin kungiyar tarayyar Afirka wato AU da za a yi a kasar Masar domin neman samun fahimta da goyon baya daga kasashen Afirka wajen warware rikicin da kasarsa ke fuskanta a yanzu.

Ran 27 ga wata, an kada kuri'a a zagaye na 2 na babban zaben shugaban kasar a Zimbabwe. Kafin wannan, dan takara daban wato shugaban jam'iyyar 'yan hamayya, wato jam'iyyar MDC Mr. Morgan Tsvangirai ya janye jikinsa. A cikin wannan hali ne kasashe da yawa suka yi kira ga Zimbabwe da ta dakatar da kada kuri'ar, amma Zimbabwe ba ta karbi wannan shawara ba, ta gudanar da kada kuri'a a zagaye na 2 a daidai lokacin da aka tsara.

Saboda kasashe da yawa sun yi shakkar halamtaccen kada kuri'a a zagaye na 2 na babban zaben shugaban Zimbabwe, shi ya sa yanzu gwamnatin Zimbabwe tana fuskantar babbar matsin lamba daga akasarin ra'ayoyin jama'a na kasashen duniya. Domin warware rikicin, Mr. Mugabe ya bayyana fatansa a bayyane na yin shawarwari da jam'iyyun 'yan hamayya, ya kuma yi kira ga jam'iyyun kasar da su yi shawarwari tare domin raya kasarsu. Ban da wannan kuma, ya jaddada cewa, yin tattaunawa a tsakanin jam'iyyu cikin sahihanci, hanya ce da za a bi wajen warware matsalar.

Ko shakka babu Mr. Mugabe ya gabatar da sharadi na farko ga jam'iyyun 'yan hamayya wajen yin shawarwari. Patrick Chinamasa, ministan dokoki na kasar ya yi bayani da cewa, ya kamata a yi shawarwari ne a tsakanin jam'iyyar da ke mulkin kasar da kuma jam'iyyun 'yan hamayya, kada sauran bangarori su tsoma baki a ciki. Ba za a yi tattaunawa kan batutuwan da ke shafar sake raba gonaki da yin shakkar gyare-gyaren da ake yi wa gonaki ba. Ban da wannan kuma, ya kamata jam'iyyun 'yan hamayya da jam'iyyar da ke mulkin kasar su hada gwiwarsu, su yi kira ga kasashen duniya da su soke takunkumin da ake yi wa Zimbabwe.

Mr. Tsvangirai bai mayar da martani nan take dangane da rokon Mr. Mugabe na yin shawarwari ba. Da farko, ya ki amincewa da sakamakon kada kuri'a a zagaye na 2 na babban zaben shugaban kasar. A ganinsa, wannan shi ne abin dariya. Mr. Mugabe ya zama shugaban kasar ne ba bisa doka ba. Daga baya, ya ce, ya amince da yin shawarwari da jam'iyyar da ke mulkin kasar, amma ba zai yi tattaunawa da haramtacciyar gwamnatin ba. Ga alama, bayanan da Mr. Tsvangirai ya yi sun yi baki biyu. Amma bisa halin da ake ciki a yanzu, tabbas ne za a yi tattaunawa a tsakanin jam'iyyar da ke mulkin kasar da kuma jam'iyyun 'yan hamayya.

Dangane da Mr. Mugabe ya zama shugaban Zimbabwe, kasashen yammacin duniya da yawa sun yi fushi sosai. Nan da nan kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya sun sanar da sanya wa Zimbabwe karin tsauraran takunkumi, za su kuma mika batun Zimbabwe ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna a ran 30 ga wata.

Game da wannan, wasu kasashe mambobin kungiyar AU suna ganin cewa, sanya wa Zimbabwe takunkumi ba zai warware rikicin da wannan kasa ke fuskanta ba, sai zai kawo wa jama'ar Zimbabwe karin wahalhalu kawai. Bisa labarin da kafofin yada labaru na Zimbabwe suka bayar, an ce, a sakamakon babban zaben shugaban kasar da ya gabata da kuma takunkumin da kasashen yammacin duniya ke yi wa Zimbabwe, yanzu tattalin arzikin wannan kasa na bakin tarbabarewa, darajar kudin kasar ta ragu sosai, yawan mutane marasa aikin yi ya karu sosai, kuma ana karancin abinci da kayayyakin masarufi. Dukkan wadannan matsaloli fararen hula na Zimbabwe su ne kawai suke fuskanta. A halin yanzu, kasashen yammacin duniya sun tsananta takunkumin da suke yi wa Zimbabwe, za su kara lalata zaman rayuwar fararen hula na Zimbabwe kawai.(Tasallah)