Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 15:35:43    
Aikin fama da girgizar kasa da gwamnatin kasar Sin ta gudanar ya zama wani abin koyi ga duk duniya

cri
A kwanan nan, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki tsauraran matakai cikin sauri kan fama da girgizar kasa bayan faruwar bala'in a lardin Sichuan na kasar, wanda ya zama wani abin koyi ga duk duniya.

Ban Ki-Moon ya yi wannan bayani ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a gabanin ziyararsa a kasar Sin. Lokacin da aka tabo ziyarar da ya yi a yankunan da ke fama da girgizar kasa na lardin Sichuan a ran 24 ga watan Mayu, ya ce, abubuwan da ya gani a yankunan da suka fi fama da bala'in ya burge shi sosai, kuma ya ji bakin ciki sabo da halin da wurin ke ciki. Amma a sa'i daya kuma, kyawawan ayyukan fama da bala'in da kuma ceton mutane da ke karkashin jagorancin shugaba Hu Jintao da firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin sun gamsar da shi sosai.

Ban da wannan kuma ya ce, ayyukan fama da bala'i da gwamnatin kasar Sin take gudanarwa wani abin koyi ne, wanda zai samar da fasahohi masu daraja ga sauran kasashen da za su gamu da bala'i daga indallahi.(Kande Gao)