---- Kwanan baya an buga da kuma sayar da littafi mai sunan "Kabilar Xibo, takaitaccen bayani kan littattafan tarihi na kananan kabilun kasar Sin", wannan littafi ya zama littafi na farko daga cikin babban littafi mai sunan "Jihar Xinjiang, takaitaccen bayani kan littattafan tarihi na kananan kabilun kasar Sin".
Tun fil azal, da akwai 'yan kabilu 13 ciki har da kabilar Uygur da Kazak da Mongolia da Hui da Xibo da Han wadanda suke zama a jihar Xinjiang, cikin 'yan shekaru nan da suka wuce, gwamnatin jihar ta yi ayyuka da yawa domin ceto da tattara da yin bincike da daidaita da yin gyara-gyare da kuma fassara littattafan tarihi, kuma daga shekarar 2000 an fara aikin shirya babban littafin tarihi game da kananan kabilu na jihar Xinjiang.
Mr. He Zhongde, mataimakin direktan ofishin addini na kwamitin kabilu na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, an shefe kusan shekaru 8 ana shirya littafi mai sunan "Kabilar Xibo, takaitaccen bayani kan littattafan tarihi na kananan kabilun kasar Sin", a gun wannan lokaci an yi hadin gwiwa a tsakanin jihar Xinjiang da birnin Beijing da larduna Liaoniing da Jilin da Heilongjiang da jihar Mongolia ta gida, an tattara tsarin ka'idodji da yawansu ya kai kusan 3000 game da litattafan tarihi na kabilar Xibo da aka samu daga duk kasar Sin baki daya, wadannan kuma sun shafi fannonin tarihi da addini da tarihin kabila da kuma adabin jama'a.
---- A ran 29 ga wata mun sami labari daga hukumar kiwon lafiya ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta cewa, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar ta kaddamar da manufofi masu gatanci da yawa don ba da kwarin gwiwa ga mata manoma da makiyaya masu juna 2 da su haifi jarirai cikin asibiti, sabo da haka yawan masu nakuda da jarirai da suka muta ya ragu sosai.
Tun shekara da shekaru da suka wuce, yawancin manoma da makiyayya masu juna 2 na jihar Tibet ba su son haifi jarirai cikin asibiti, sabo da haka da akwai masu nakuda da jarirai wadanda suka muta sabo da wuyar haihuwa. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Tibet ta dauki manufar nuna gatanci ga masu nakuda cewa, a lokacin da mata manoma da mikiyaya masu juna 2 suke kwance a cikin asibita domin haihuwa, za a maida musu dukkan kudaden da suka kashe in sun gabatar da rasidin kudin da suka kashe kan jiyya. Sa'an nan kuma an ba da kyautar tufafin jariri kwat daya ga kowace mai nakuda da ta haifi jariri cikin asibiti, kuma an maida mata da kudin asibiti da na sufuri domin zuwa da dawowa daga asibiti bisa risidin kudin da suka gabatar.(Umaru)
|