
Yau 30 ga wata, da misali karfe 9 na safe ne, aka fara yin bikin mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Wuzhong da ke jihar NingXia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta a yammacin kasar Sin.

An fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a makarantar midil ta Wuzhong, kuma tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar zai kai kilomita 5.6, masu dauke da wutar su 193 sun shiga cikin wannan biki. A kan hanyar mika wutar wasannin Olympic na Beijing, za a bi hanyar gabas ta Mingzhu da hanyar Kaiyuan da titin yamma na Shengyuan da dai sauran shahararrun wurare, a karshe dai za a isa wuri na karshe watau dandalin Shengyuan.(Bako)
|