Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-29 20:26:30    
Hukumomi na matakai daban daban na Sin sun bayar da kudin Sin RMB sama da yuan biliyan 54.7, don yaki da bala'in girgizar kasa

cri
Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da rahoto cewa, ya zuwa ranar 29 ga wata da karfe 12, hukumomi na matakai daban daban na kasar Sin sun bayar da kudin da yawansu ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 54.716, don yaki da bala'in girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.

Kuma ya zuwa ranar 29 ga wata da karfe 12, mutane 69,195 ne suka rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa, yayin da 18,404 suka bace.

Ya zuwa ranar 29 ga wata da karfe 12 kuma, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da ke da darajarsu ta kai kudin Sin yuan sama da biliyan 54.9 daga bangarori daban daban na gida da na waje, kuma an riga an bayar da taimakon kudi da na kayayyaki da darajarsu ta kai kusan yuan biliyan 20 ga yankuna masu fama da bala'in. (Bilkisu)