Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-29 18:49:58    
Madam Rice ta yaba wa ayyukan da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suke gudanarwa wajen tinkarar girgizar kasa

cri

A ran 29 ga wata da yamma, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Condoleezza Rice ta kammala ziyararta a yankunan girgizar kasa na lardin Sichuan, ta tashi zuwa birnin Beijing, Madam Rice ta yaba wa ayyukan da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suke gudanarwa wajen tinkarar girgizar kasa.

A lokacin da bai fi awoyi hudu ba da take ziyara a lardin Sichuan, Madam Rice ta fahimci zaman rayuwar jama'ar da ke fama da girgizar kasa, ta yi magana da likitoci da ke aiki a tashoshin likitanci, ta kalli shirye shiryen wake wake da raye raye da yara suka yi mata, ban da wannan kuma, Madam Rice ta bayar da littattafai a matsayin kyauta ga yaran.

A gun taron manema labaru na gida da na waje, Madam Rice ta yaba wa ayyukan da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suke gudanarwa wajen tinkarar girgizar kasa. Madam Rice ta ce, tana mamaki sosai domin kasar Sin tana maido da ayyuka da sake gina gidaje a yankunan girgizar kasa da sauri har haka, ta hakan ne, ta ga girman jama'ar kasar Sin.(Danladi)