Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-29 17:37:47    
Hongkong, da Macau za su shiga ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan

cri
Jiya 28 ga wata da dare, gwamnan yankin musamman na HongKong Mr. Donald Tsang, da takwaransa na Macao, Mr. Edmund Ho Hau Wah, sun bayyana cewa, yankunan biyu za su shiga ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan.

A wannan rana, Mr. Donald Tsang, da Mr. Edmund Ho Hau Wah, sun shugabanci kungiyoyin wakilai na Hongkong da Macau, da kuma yi shawarwari tare da shugabannin lardin Sichuan, inda suka tattauna kan ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, bayan haka kuma, sun yi bincike a wasu yankunan da suka fi fama da bala'in.

A gun wani manema labaru da aka shirya a birnin Chengdu, Mr. Donald Tsang ya bayyana cewa, Hongkong zai bayar da taimako kan gundumomin da suka fi fama da bala'in, kuma zai halarci aikin sake gina sansanin panda da ke Wolong. Mr. Edmund Ho Hau Wah ya bayyana cewa, a cikin kasafin kudinta na shekaru biyar masu zuwa, gwamnatin yankin musamman na Macau za ta bayar da kudin musamman, don nuna goyon baya ga ayyukan sake raya yankunan masu fama da bala'in na lardin Sichuan. (Bilkisu)