Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-29 17:13:53    
Madam Rice ta isa birnin Chengdu domin fara yin ziyara a kasar Sin

cri

Bisa gayyatar da ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Yang Jiechi ya yi mata, a ran 29 ga wata da safe, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Condoleezza Rice ta shugabanci tawagar wakilai da ke kunshe da mutane fiye da 60 sun isa birnin Chengdu, domin fara yin ziyarar da za a shafi kwanaki biyu ana yinta.

A gun ziyararta a lardin Sichuan, Madam Rice za ta je Dujiangyan, domin nuna jejeto ga jama'ar da aka tsugunar da su, da kuma yin rangadi kan aikin tsabatar da ruwa da kasar Amurka ta bayar a matsayin kyauta, haka kuma za ta halarci taron manema labaru na gida da na waje.

Madam Rice za ta tashi zuwa birnin Beijing a ran 29 ga wata da yamma. A gun ziyararta a birnin Beijing, shugabannin kasar Sin za su gana da Madam Rice, Yang Jiechi zai yi shawarwari da ita. Bangarorin biyu za su yi musanyar ra'ayoyinsu kan manyan lamuran duniya da shiyya shiyya, wadanda suke jawo hankulansu.(Danladi)