Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-29 17:08:05    
An kammala aikin mika wutar gasar wasannin Olympics na Beijing na rana ta farko a jihar Ningxia

cri

A ran 29 ga wata, An kammala aikin mika wutar gasar wasannin Olympics na Beijing na rana ta farko a jihar Ningxia ta kabilar Hui da ke da ikon tafiyar da harkokin kanta.

Zango da aka mika wutar yola ta rana ta farko a jihar Ningxia shi ne birnin Zhongwei. Da misalin karfe 8 na safe, an fara mika wutar yola, mai dauke da wutar yola na farko shi ne shahararren marubuci na kasar Sin Mr. Zhang Xianliang.

Duk tsawon hanyar mika wutar ya kai kilomita 17.96, masu dauke da wutar yola da yawansu ya kai 208 sun shiga cikin wannan aiki.

A bikin fara mika wutar yola da aka shirya a ran nan, dukkan jama'ar da suka shiga cikin aikin mika wutar sun nuna jimami har na tsawon minti daya, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamkon girgizar kasa a gundumar Wenchuan. Ban da wannan kuma, sun bayar da kudin kyauta ga yankunan girgizar kasa.

A ran 28 ga wata a birnin Sharm el-Sheik, ministan harkokin waje na kasar Masar Mr. Ahmed Abul Gheit ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta birnin Beijing ta shekarar 2008 za ta zama wata kyakkyawar dama da 'yan wasa na kasashen duniya su ji dadi tare, kuma su taya murnar zaman lafiya da kauna tare.(Danladi)