Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-27 16:20:40    
Waiwaye adon tafiya(8)

cri

Lubabatu:Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a filinmu na amsoshin wasikunku, inda yau za mu ci gaba da gabatar muku shirinmu na "waiwaye adon tafiya", wato shirin musamman na murnar cika shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, a cikin shekaru 45 da suka wuce, sashen Hausa ya kulla zumunta da masu sauraronsa da yawa. Dimbin masu sauraronmu sun shafe shekara da shekaru suna sauraronmu. Kwanan baya, wakilinmu Bello ya je Abuja, ya sami damar hira da wani tsohon mai sauraronmu da ke wurin, to, a cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku hirar da muka yi da wannan tsohon amininmu, wato malam Salisu Muhammed Dawanau, wanda ya yi shekaru fiye da 20 yana sauraronmu.

Bello:Malam Salisu, sannu.

Salisu:Yauwa,sannu kadai.

Bello:Na ji dadin samun damar hira da kai, da farko dai, ko za ka gabatar da kanka ga masu sauraronmu.

Salisu:Ni dai sunana Salisu Muhammed Dawanau, ma'aikacin gwamnati ne a nan Abuja, asalina mutumin Dawanau ne, jihar Kano, amma na taso a garin Akwanga, jihar Nasarawa, kuma yanzu haka, ina zaune a Abuja, ina aiki a nan Abuja

Bello:Tun yaushe ne ka fara sauraron sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin?

Salisu:Alal hakika, na fara sauraren shirye-shiryen sashen Hausa na rediyon kasar Sin a karshen shekarar 1987, a cikin shekarun da na yi sauraron gidan rediyon, na fahimta sosai, na kuma ilmantu, na tabbata sauran masu sauraronsu, wadanda suka fara saurare, ko dai kafin ni, ko baya na, su ma, ina da tabbacin, sun ilmantu, sun fahimci shirye-shiryensu, musamman sabo da fadin gaskiya da suke yi, da kuma shirye-shirye masu kayatarwa.

Bello:A lokacin da ka fara sauraronmu, ka kasance a cikin firamare?

Salisu:A'a, ina karatu a makarantar gaba da firamare, lokacin da ya rage mana shekara kamar daya mu kare, na fara sauraron gidan rediyon, musamman ma sashen Hausa,

Bello:Ta wace hanya ce ka san gidan rediyonmu?

Salisu:Hakika, akwai wani amininmu, kuma surukinmu, dan uwanmu, kuma zan ce, yayana, Salihu Makanika Mota, a garin Akwanga, ta dalilinsa, na fara sauraron sashen Hausa. Don a lokacin, mu kan je gidansa, kuma na kan ga takardu na game da sashen Hausa, sai na nuna sha'awata game da gidan rediyo, daga nan ne dai, ta dalilinsa, na fara sauraron sashen Hausa.

Lubabatu:A cikin wasikar da ya turo mana, malam Salisu ya ce, "Hakika, ina sauraren sashen Hausa na CRI ne musamman saboda samun labarai masu kayatarwa da kuma labarai masu dauke da gaskiya wadda masu iya magana kan ce "ciki da gaskiya wuka baya hudawa".

Yawa-yawan masu saurarenku musamman wadanda na zanta da su, a da can baya da kuma cikin kwanakin nan, sun sanar da ni cewa "a wannan karni, yana da wuya ka sami gidan rediyo mai yada labarai na gaskiya kamar sashen Hausa na CRI". Ashe ke nan, yabon gwani ya zama dole. Dole in yaba muku a ko da yaushe."

Bello:Mene ne da ke cikin shirye-shiryenmu ya jawo hankalinka, har ya sa ka fara sauraron shirye-shiryenmu?

Salisu:Da can baya, kafin in fara sauraron gidan rediyon kasar Sin, musamman sashen Hausa, na kan saurari labaransu, kamar sashen Hausa na VOA da BBC da dai sauransu, sa'an nan mu kan kalli kafofin yada labarai, musamman telebijin na yammaci da na Turai, to, sai na lura, shirye-shiryensu, musamman wanda yake na kasar Sin, yana da bambanci da wanda na saurara a gidan rediyon, sai na ga kafofin yada labarai na yammaci kamar an dan gurbata shi, sai na ga gidan rediyon kasar Sin din nan, kamar tsantsan ainihin abin da ke faruwa a kasar Sin, sai na ga ya fi dacewa, in rika sauraronsu, musamman in dai labarin ya danganci kasar Sin ne, don an ce, da dan gari a kan ce gari, ya kamata mutum ya sami labari daga ainihin inda ya fito. Ba ta jita-jita ba.

Bello:Ko wace rana kana sauraro ba?

Salisu:E, ba shakka, in ban saurara a ainihin lokacin da a kan yi ba, washegari, na kan duba a internet, in ga abin da ya dace in karanta, na kan yi printing daga internet, in karanta.

Bello: A cikin shirye-shiryenmu, me ka fi so?

Salisu:Alal hakika, akwai bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, ta hanyar wannan shiri na bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, ba ma na tattalin arziki kawai ba ne, na aihinin yadda kasa da al'umma ke kan ci gaba ne. Kuma ta sauraron wannan shiri, na kan fahimci yadda kasar Sin da mahukuntan kasar su kan tafiyar da al'amuransu yadda al'ummarsu za su karu, ina son wannan shiri sosai. Sai kuma shirin amsoshin wasikunku, don ta wannan shiri, ko ban saurari an karanta wasikata ba, na kan saurari na wasu, in ji ra'ayoyinsu game da shirye-shiryen sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin.

Lubabatu:Ban da sauraron muryar da ta zo daga kasar Sin, malam Salisu shi da kansa ya taba sa kafarsa zuwa can bangon duniya, wato a shekarar 2001, bisa gayyatar da gidan rediyon kasar Sin ya yi masa, inda ban da ziyara a wurare da dama masu ni'ima da tsawon tarihi da kuma karuwa da abubuwan da ya gani, malam Salisu ya kuma hadu da ma'aikatan sashen Hausa, wadanda da ma muryoyinsu ne kawai yake ji.

Bello:Na san cewa, ka taba zuwa kasar Sin, ko za ka bayyana mana ziyararka a kasar Sin?

Salisu:E,to, na sami damar zuwa kasar Sin sanadin gasar kacici-kacici da aka shirya a shekarar 2001, kuma sunan gasar shi ne "Ni da gidan rediyon kasar Sin". Da na rubuta, bayan 'yan watanni, sai Allah ya sa na yi nasara, ba domin na fi sauran masu sauraro sanin yadda ake rubutu ba, a'a, Allah ne ya ba da nasara, sa'an nan, na samu na tafi can.

Bello:Masu sauraronmu za su so ka bayyana musu abubuwan da ka gani a kasar Sin?

Salisu:Da farko dai, bayan da muka sauka a filin jirgin sama, aka kai ni hotel, bayan da na ci abinci, ita malama Halima ta tambaye ni, wuraren da nake so in tafi a kasar Sin. Na gaya mata, wurin farko dai, babbar ganuwa, sabo da na dade na kan ji labarin babbar ganuwa, kuma na kan gani a telebijin, na kan kuma karanta, wurin da na fara zuwa ke nan, muka tafi, muka yawata, daga can kashegari muka tafi garin Shijiazhuang da ke cikin jihar Hebei, amma kafin mu tafi, a nan Beijing mun je wurare su Beihai Park, da wasu wurare masu muhimmanci kuma tsawon tarihi. Gaskiya na yi farin ciki da tafiyata, kuma na ilmantu, na gane abubuwa da dama da da ban gane su ba.

Bello:ko ka iya tunawa da abin da ka ji rai lokacin da ka gamu da su mutanen sashen Hausa a karo na farko, sabo da da ma, ba ka taba ganinsu ba, sai sauraron muryoyinsu?

Salisu:Gaskiya, na yi farin ciki sosai, farin ciki wanda ba zan iya kwatanta girmansa ba, ba zan iya misalta shi ba, musamman ma ban taba zuwa kasar Sin ba, Allah ya nufa ta sauraronsu ne na tafi kasar Sin, kuma abin farin ciki na ga mutanen din wadanda muryoyinsu kawai nake ji, kuma na gansu, na aminta wadannan mutanen da na gani mutane ne masu karimci da son baki. Musamman da yake haduwan da muka yi da su gaba daya a cikin ofishinsu, a lokacin, akwai malam Usman, akwai su malam Aliyu, da sauransu, kuma a gaskiya, yadda na ga tsarinsu a sashen, duk wanda ya zauna tare da su, ko da awa guda ne, in ya bar wurin, zai yi begensu, sabo da ba za ka ji kome ba, sai labarin 'yan uwantaka da aminantaka.

Lubabatu:A cikin wasikarsa, malam Salisu ya ce, "na nuna sha'awa kwarai ga abubuwan da suka zo daga kasar Sin musamman fina-finai masu nasaba da yake-yake da jarumtaka da sarakuna da magabata da kuma wasu mutanen kasar Sin ke nuna wa. Haka kuma, da wasu kayayyakin cin abinci irin su cokala da kwanuka da farantai da dai sauransu wadanda suke da kwari da kuma inganci, wasu abokaina har sun sa mini suna 'Mr. CHINA'."

Bello: A cikin wasikarka, na ga da ka koma Nijeriya, yanzu wasu abokanka suna kiranka "Mr.China", shin me ya sa suke kira ka haka?

Salisu:To, ba a rasa nasaba da ko da yaushe sun ga wani littafi an nuna, ko wata mujalla, ko jarida, da an duba, sai a ga mai yiwuwa, labari ne da ya danganci kasar Sin da mutanen Sinawa, dalilin da ya sa ke nan wasu abokaina ke kira na hakan din.

Lubabatu:To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, amma kada ku manta, a makon gobe war haka, za mu ci gaba da kawo muku shirye-shiryenmu na "waiwaye adon tafiya", da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, "sai Allah ya kai mu ranar Jumma'a mai zuwa. (Lubabatu)