Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-27 12:14:02    
An fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Datong da ke lardin Shanxi a kasar Sin

cri

Yau 27 ga wata, an fara yin bikin mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 a birnin Datong da ke lardin Shanxi a tsakiyar kasar Sin.

Birnin Datong shi ne zango na uku da za a yi bikin mika wutar wasannin Olympic a lardin Shanxi, haka kuma shi ne zango na karshe a wannan lardin, tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar wasannin Olympic a birnin Datong zai kai kilomita 12, masu dauke da wuta 208 za su shiga cikin wannan biki. Tian Lijun wani injiniya na wurin hakowar kwal na Xinzhou na kamfanin haka kwal na birnin Datong zai zama mai dauke da wuta na farko, haka kuma zakarar gasar wasannin fi da gwani wajen gudun kan kankara na Figure Skating da aka yi a shekarar 2006 Pangqing da Tongjian su ma za su shiga cikin wannan bikin.

Wuri na farko da za a fara yin biki mika wuta shi ne dandanlin lafiya na wurin hakowar kwal na Jin huagong na kamfanin haka kwal na birnin Datong, kuma ya bayyana mana muhimmin matsayi na sana'ar hakowar kwal a birnin Datong da kuma dukkan kasar Sin baki daya, wuri na karshe wajen mika wutar wasannin Olympic na Beijing shi ne dandanlin kogon duwatsu na Yungang na 20 watau abubuwan al'adu da muka gaji daga kakanin-kakaninmu na duniya.(Bako)