Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-26 16:55:26    
Wani malamin koyarwa na kasar Amurka a Sin

cri

Wannan malamin koyarwa na kasar Amurka sunansa shi ne Joseph Barbarise, yana da shekaru 55 da haihuwa a wannan shekarar da muke ciki. Shi dan daukar hoto ne. ba tsammani ba zato ya samu damar aiki a kasar Sin a matsayin malamin koyarwa a jami'ar aikin gona ta lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin

Mr Joseph shi mutumin ne na jihar Florida ta kasar Amurka,ya taba aiki a matsayin mai daukar hoto, yana kaunar yawon shakatawa sosai. Daga cikin kasashe da nahiyoyin da ya sa kafa, Joseph ya fi kaunar kasashen Asiya. Ba zato ba tsammani da ya shiga shafuna dangane da mutanen kasar Sin a yanar gizo ta internet,abin da ya gani ya dauka hankalinsa. ya ce" na yi shekara daya na yi mu'amala da mutanen Sin ta yanar gizo ta internet, ina jin haka mutanen Sin suna da kirki da fara'a su kan nuna aminci ga baki. Saurin ci gaban da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arzkin kasa ya burge ni kwarai da gaske. Shi ya sa na daura niyyar zuwa kasar Sin. Na sayar da gidana da motata a kasar Amurka, na yi murabus daga aikina. Ina tsammani in yi zama da bai wuce wata daya ba a kasar Sin, ina yawon bude ido ina daukar hotuna."

Da haka a yanayin zafi na shekara ta 2006, Joseph shi kansa ya zo nan kasar Sin. Bai yi tsammanin zama cikin dogon lokaci a kasar Sin ba, ya samu gurbin aiki na malamin koyarwa na turanci a wata jami'a. Tare da goguwar da ya ke yi a kasar Sin,Joseph ya kara kaunar kasar Sin. A ganinsa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta samar da kyakkyawar makomar samun ci gaba ga baki, mutanen kasar Sin su kan nuna aminci ga baki, shi ya sa baki suna jin tamkar sun dawo gida. Da ganin haka joseph ba ya so ya bar kasar Sin ba. A gabannin ranar bikin krista ya kuduri aniyar yin wani abu mai ma'ana domin taimakon mutanen kasar Sin da suka ba shi taimako

Ya ce"bayan da na sauka a kasar Sin, abokan aikina na kasar Sin sun nuna aminci sosai, sun ba ni taimako da sa kulawa masu yawa. Ina so in ba da taimako ga wani iyalin dake bukatar taimako a gabannin ranar bikin Krista in kawo masa alheri, a sa'I daya kuma in yi musu bayani kan ranar bikinmu ta Krista. Na sani ba na iya ba da taimako ga dukkan mutanen ba,amma in yi iyakacin kokarina in ba da taimako ga wasu."

Bisa taimakon abokan aikinsa, Joseph ya kulla aminci da wani iyali mai suna Feng dake cikin yankin duwatsu na birnin Xinmi a lardin Henan. Joseph ya ce har abada a duk rayuwarsa ba zai manta da ranar biki ta krista ta shekara ta 2006 ba. Dalili kuwa shi ne daga wannan lokaci ya shiga wani iyalin dake zama cikin duwatsu, kuma ya hada kansa da zaman wannnan iyali. Da akwai yara biyu a cikin wannan iyali mai suna Feng. Daya ana kiranta Feng Xiaoyan dayan kuma ana kiransa Feng Xiaolei,garayu ne da suka rasa iyayensu. Kafin shekaru biyu da suka shige, ubansu ya rasu bisa sanadin cuta,uwarsu ta bar gida ta gudu,sai kakaninsu mai yawan shekaru ne ya dau nauyin kula da iyali. Daga nan kane Xiao Lei ko murmushi ma ba ya yi. Joseph ya tuna da cewa  "Karo na farko da na ga yaro Xiao Lei babu murmushi ko kadan a fuskarsa. Da ya karbi kyauta, idanunsa na da sanyi sanyi. Bayan da na yi tambayar kawarsa, na sane da cewa shi yaro ne mai fara'a a da, sauyin iyalin ya kawo masa lahani mai tsanani. Ina so in shiga duniyarsa in mayar da shi ya koma yadda yake a da, ina so in mayar da murmushin da ya bace a fuskarsa."

A ranar bikin Krista ta shekara ta 2006, Joseph ya kawo wani akwatin da ke dauke da sabbin tufafin sanyi da wasu kayayyaki na zaman yau da kullum da kuma abinci da kudade.Tun daga wannan lokaci kowane wata ya kan je gidan yara domin duba yadda suka yi zama, ya kuma ba su kayayyaki na karatu da na wasan yara. Bisa taimakonsa da kulawa da ya sanya, murmushi ya dawo fuskokin yaran, sun sake nuna fara'a da kara imani A cikin wata wasikar da Xiao Lei ya aika wa Joseph, Xiao Lei ya bayyana cewa tabban ne zai yi iyakacin kokarinsa wajen karatu da zama wani mutum da ya yi tamkar Hoseph wanda ya yi farin ciki da ba da taimako ga saura. Tare da kauna zai ba da taimako ga matalauta kamar shi domin mayar da martani ga wadanda suka ba ni taimako.

A cikin gudanarwar da ya ke yi na mu'amala da iyali mai suna Feng, kaunar Joseph kan wannan iyali ta kara karfi. Da farkon farko, ya yi shirin kawo wa wannan iyali abin alheri,amma yanzu a ganinsa wani nauyi ne da ya kamata ya dauka a wuyansa na ba da taimako ga wannan iyali a duk rayuwarsa.

Da ya samu labarin makarantar da yaran ke karatu a ciki na bukatar kayayyakin aikin koyarwa cikin gaggawa da littattafai, Joseph ya shirya ayyukan sayarwa a harabar jami'ar aikin gona ta lardin Henan ko a waje da ita, ya saye kayayyakin koyarwa masu aiki da wutar lantarki domin makarantar kuma ya taimaka wa makaranta wajen kafa dakin littattafai. Wata rana da wata motar lorry dake dauke da kayayyakin koyarwa ta isa makarantar firamare dake cikin duwatsu, shugaban makarantar mai suna Liu Guanjun ya girgiza har hawayensa na zuba.Ya ce  "Mr Joseph ya baiwa 'yan makarantarmu taimakon kudi, na yi masa godiya. Na girgiza da na ganin wani bakon da ya zo nan kasar Sin ya ba da taimako ga iyali da shi bai sani ba a da, ya isa abun misalin koyo. Da na gani haka, hawayena ya zuba in yi musu godiya."

A cikin shekara daya da 'yan kai bayan haka, taimakon kudin da Joseph ya baiwa iyali Feng ya wuce kudin Sin Yuan dubu goma,littattafan da kayayyakin koyarwa da ya baiwa makarantar a matsayin kyauta sun yi yawan gaske. A halin yanzu mutanen kauyen da Xiao Yan da Xiao Lei ke zama a ciki sun zama aminan Mr Joseph, duk lokacin da aka samun labarin zuwansa a kauye, manya da kanana tsofafi da yara na kauyen sun fita waje sun yi masa maraba kuma suna neman yin musafha da shi. Mr Joseph ya yi farin ciki da ya sami kansa a cikin wannan yanayi. Joseph ya ce" mutanen kauye sun nuna mini aminci sosai,su mutane masu fadin gaskiya da kirki, sun ba ni abubuwan mafiya daraja na iyalansu. Ina jin kamar na koma gidana."

Mr Joseph ba ma kawai ya samu kauna daga 'yan makaranta ba sabo da aikin nagarta da ya yi, kuma ya kawo tasiri ga abokan aikinsa. Lu Xinying, wata ma'aikacciyar aiki ta Mr Joseph a kasar Sin, ta ce a kan matsayin abokiyar aikin Joseph ta koyi abubuwa da dama daga wajen Mr Joseph. Ta ce "A cikin shekara daya da rabi da Mr Joseph ya zo makarantarmu a matsayin malamin koyarwa,ya mai da hankalinsa wajen aikin koyarwa, ya samu kauna daga 'yan makaranta, ya kuma ba da taimakonsa ga wadanda suke bukata wajen kudi ko jini,lalle ya isa abun misalin koyo. Amma wasunmu ba su kai yadda Joseph ya yi ba watakila sun ga 'yan makaranta dake bukatar taimako suna so su yi wani abu.Mr Joseph dan Amurka ne bayan da ya yi aiki a kasar Sin ya ba da taimako ga yaran iyalan dake fama da talauci,kuma ya ba da taimakonsa ga sauran mutanen Sin,ya yi babban aiki."

A shekara ta 2007, gwamnatin lardin Henan ta kasar Sin ta bayar da lambar zumunci ta rawayan kogi wadda aka baiwa aminanmu na duniya, da kwararru na kasshen ketare da sinanan kaka gida da mashahuran mutane na Hongkong da Macao da suka ba da babban taimako wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban zamantakewa na lardin.

Har wa yau dai yawon bude ido wani muhimmin aiki ne maras makawa a zaman rayuwa na Mr Joseph. A cikin shekara daya da rabi da suka shige, ya sa kafarsa a kowane lungun kasar Sin. Ya ce abubuwan da ya gani a ziyararsa sun burge shi kuma har abada ba zai manta da su ba. Ya ce"Na hau babbar ganuwar kasar Sin, na ji al'adu mai tarin yawa da tarihi na tsawon shekaru dubu biyar na kasar Sin. Na girgia da ganin wadannan ayyukan tarihi. Mutum mutumin sojoji da dawaki da na gani dab da birnin Xi'an, abin mamaki ne na duniya,kuma wani babban aiki ne. Kwarin Jiuzaigou yana da kyaun gani sosai ya burge ni kwarai da gaske, koguna da duwatsu a wurin Guilin har abada ba zan iya manta da su ba. Na je wurin nan ne a yanayin hunturu na shekarar bara,babu sauran masu yawon bude idanu sai ni daya kawai. Babu motsi,babu kukan tsuntsaye, babu kara ko kadan,sai bugun zuciyata kawai,na ji dadin zama a cikin wannan yanayi."

Mr Joseph ya ce ya sa kafa a kasashe da dama a duniya, kasar da ta fi ba shi sha'awa ita ce kasar Sin. Ya yi farin ciki da zabar kasar Sin da ya yi,yana so ya ci gaba da zama a kasar Sin.