Ran 26 ga wata a nan birnin Beijing, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta shirya liyafa domin nuna godiya ga kasashen waje bisa taimakon da suka baiwa kasar Sin wajen tinkarar bala'in girgizar kasa. Mr. Li Keqiang mataimakin firaminista kuma mataimakin kwamanda na babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya halarci wannan liyafa kuma ya yi jawabi.
Mr. Li Keqiang ya ce, yayin da kasar Sin ke fama da bala'in girgizar kasa, kasashen duniya sun ba da taimakon kudi da kayayyaki da yawa ga kasar Sin, kuma wasu kasashe sun aika da kungiyoyin ceto da kungiyoyin ba da agaji zuwa wuraren da ke fama da bala'in, sun ba da gudummawa sosai ga kasar Sin wajen tinkarar bala'in, wannan ya nuna amincewa da ainihin jin kai na jama'ar kasa da kasa. Gwamnati da jama'ar kasar Sin ba za su manta da wannan ba har adaba.
A wannan rana, jami'an jakaddanci na kasashen waje da wakilan kungiyoyin kasa da kasa fiye da 170 sun halarci wannan liyafa.
Ya zuwa yanzu, akwai kasashe fiye da 160 da kungiyoyi 10 na kasa da kasa sun ba da taimakon kudi da kayayyki ko aika da mutane ga kasar Sin.
|