Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-26 16:51:28    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Asalam alaikum jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkammu da sake saduwa da ku a cikin wannan sabon shiri na "labaru masu ban sha'awa na kasar Sin", muna fatan kuna jin dadin shirin nan.To sai ku kutso akwatunan rediyonku ku saurara:

"yan ci rani sun zama abun misalin koyi a birnin Shijiazhuang na lardin Hebei. An sami 'yan ci rani guda shida,yawancinsu sun zo ne daga lardin Zhejiang da aka daukaka su a matsayin mazauna masu kirki na birnin Shijiazhuang,babban birnin lardin Hebei na kasar Sin saboda suka ceci yara guda biyu daga wani kogin da ya daskare. A ran 30 ga watan Janairu na wannan shekarar da muke ciki da jin kukar yara,nan da nan 'yan ci rani guda biyu sun yi tsalle cikin ruwan kogin da ya daskare sun kama yaran da suka nutsa cikin ruwan kogin,sauran 'yan ci rani guda hudu dake kan kankara sun bayar da taimakonsu ga wadanda suka ceci yara. Daga baya aka fitar da yaran biyu daga kogin,aka kai su asibiti da ba su magani cikin lokaci.Iyayen yaran sun gode wa 'yan ci rani da suka ceci yaransu kuma sun yi musu yabo kan namijin kokarin da suka yi.

An yi wa tagwaye fida domin raba su. An sami tagwaye biyu da jikinsu a hade yake a birnin Chongqing dake karkashin mulkin gwamnatin tsakiya kai tsaye.bayan da aka yi musu fida sun rabu da juna. A ran 7 ga watan Fabrairu na bana, an haifi jarirai tagwaye biyu, ba zato ba tsammani daya daga cikin tagwayen ya ji rauni dalili kuwa shi ne domin likitoci ba su jarirai biyu a hade suke. A ran 14 ga watan Fabrairu likitocin asibiti sun yi jariran fida domin taimakonsu.Kome na tafiya yadda ya kamata.aikin fida ya dau sa'o'i biyu,jariran kuma suna cikin yanayi mai kyau.

Wani tsoho ya yi yunkurin kashe aurensa. Wani tsoho mai yawan shekaru sama da sittin ya yi yunkurin kashe aurensa cikin shekaru 40 da suka shige.ya ce yana da sabani mai tsanani tsakaninsa da matar,su kan yi cacar baki dare da rana,kuma suna ta zargin juna.Daga baya tsohon ya kai karar matarsa a gaban kotu, kotun ta shiga tsakaninsu ta yi lallashi daga baya sun yarda ba za su kare aure ba.Wani alkalin da ya sa hannu kan batun nan ya ce "tsofaffin nan biyu suna kaunar juna kuma suna kulawa da juna,suna cacar baka ne kan kanana abubuwa marasa muhimmanci,shi ya sa mun shiga tsakani mun daidaita batun yadda ya kamata."

Wani mutum mai ciwon kansa na jini ya shere jama'a a kan yanar internet. An sami wani mutum da ake kiransa Luo Yuanlan wanda ya ke da shekaru 25 da haihuwa a birnin Chengdu,babban birni na lardin Sichuan dake tsakiyar kasar Sin ya kan shirya wasanni da samar da bayanai masu ban sha'awa domin shere jama'a da kuma saukaka wahalar da ya sha sabo da yana fama da ciwon kansa na jini.A watan July na shekara ta 2007 aka gano shi yana kamu da ciwon kansa na jini da jin labarin sai baki ciki ya rufe shi. Daga baya ya dau niyyar bin ra'ayin fara'a ya fara shirya wasanni da samar da bayanai masu ban sha'awa domin shere jama'a a yanar internet. Da mutane masu dimbin yawa suka karanta wasanni da bayanan da ya rubuta sun girgiza kan yunkurin da ya ya na fama da ciwon cancer na jini.

Mai kyanwa ya sanya matacciyar kyanwa a cikin firji. An sami wani mutum dake da shekaru talatin da haihuwa a birnin Shanghai,birnin da ya fi samun cigaban masana'antu a kasar Sin wanda ya yi bakin ciki kwarai da gaske sabo da kyanwan da ya kiwo ta mutu,daga baya ta dau niyyar sa matacciyar kyanwa a cikin firji domin tanada shi. Sunan mutum nan shi ne Han Yun. Ba ya so a kone kyanwa da ya kiwo na tsawon shekaru sama da goma bayan da ya ganama idonsa yadda aka kone wasu matattun kyanwoyi gaba daya. Wani amininsa ya ce bayan kyanwarsa ta mutu,Malam Han ba ya saje da mutane. Wani masani ilimin kwakwalwa mai suna Wang Yuru ya ce da akwai hanyoyi da dama na nuna baki ciki,kamata ya yi a amince da su idan ba su jawo lahani ga saura ba.

Wani malami ya la'anci kamfanin dabi. An sami wani babban malami a yankin Jinshan na birnin Shanghai da ya kai suka ga wani kamfanin dabi da ya yi kuskure na rubutu da grammar 89 a cikin wata mujjalar dauke da bayanai na ko wane copy. Galibi dai ana sayar da mujjaloli ne ga 'yan makarantun sakandare.Kamfanin dabin ilimi na lardin Jiangsu ne ya buga mujjalar.wannan malamin ya fadakar da kamfanin da ya kara sa hankali a cikin ayyukansa.

Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na labaru masu ban sha'awa. Muna fatan za mu sake saduwa da ku a wannan lokaci na mako mai zuwa.(Ali)