Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-25 19:37:26    
Kasar Sin ta yi shirin canza sunan 'dokar kula da harkokin kadarorin gwamnati' zuwa 'dokar kula da kadarorin gwamnati a masana'antu

cri

Yanzu hukumar kafa doka ta kasar Sin wato zaunannen kwamitin babban taron wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC tana gudanar da taro, inda aka yi shirin canza sunan 'shirin dokar kula da kadarorin gwamnatin kasar Sin' da ake duddubawa zuwa 'shirin dokar kula da kadarorin gwamnati a masana'antu'. Za a sa ido da kula da kadarorin gwamnati a masana'antu masu jarin gwamnatin Sin. Ko da yake an yi shirin canza sunan shirin dokar, amma an kafa shi ne domin tabbatar da tsaron kan kadarorin gwamnatin da kuma hana yin hasarar kadarorin gwamnatin, haka kuma an tsara shi ne domin nan gaba.

Kididdigar da aka samu ta nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2006, yawan kadarorin masana'antun mallakar gwamnatin Sin da ba na kudi ba, ya kai misalin kudin Sin yuan biliyan dubu 29. Bisa dokar kula da kadarorin gwamnatin Sin, za a kiyaye da kula da wadannan kadarori masu tarin yawa. An shigar da wannan doka cikin shirin kafa doka a shekarar 1993. A rabin shekarar da ta gabata, hukumar kafa doka ta kasar Sin ta sha yin nazari da tattaunawa. Bayan da ta saurari ra'ayoyin bangarori daban daban, ta yi wasu muhimman gyare-gyare kan shirin dokar, ciki har da canza sunansa. A gun taron zaunannen kwamitin NPC da aka yi a ran 24 ga wata, Hong Hu, mataimakin darektan kwamitin dokoki na NPC ya yi karin bayani da cewa, dalilin da ya sa aka canza dokar shi ne domin aiwatar da wannan doka yadda ya kamata a masana'antu. Ya ce,'A cikin shirin dokar, an fito da kayyadewa a fannonin kiyaye hakkin kadarorin gwamnati a masana'antu da tabbatar da tsaron kadarorin gwamnati da kare darajar kadarorin gwamnatin da kuma samun riba daga yin amfani da su. Yanzu an riga an ilmantar da mutane ma'anar kadarorin gwamnati da ke cikin masana'antu, shi ya sa ya fi cancanta da a canza sunan shirin dokar zuwa 'dokar kula da kadarorin gwamnati a masana'antu'.'

Daya daga cikin abubuwan da suka fi jawo hankali a cikin shirin dokar shi ne yadda za a tabbatar da tsarin sa ido da kula da kadarorin gwamnatin kasar Sin. Shirin dokar ta kayyade cewa, a cikin dukkan masana'antu masu jarin kasar Sin, ya kamata gwamnatin Sin ta sauke nauyin da ake danka mata tamkar mai zuba jari, ta mallaki muhimmin iko a fannonin samun riba da yanke muhimmiyar shawara da kuma zaben mai tafiyar da masana'antu, sa'an nan kuma, gwamnatin ta iya zaben kwamitin sa ido da kula da kadarorin gwamnatin kasar Sin da ya gudanar da aikin. A daidai lokacin da aka shigar da wannan shirin doka cikin matakin kafa doka ba da dadewa ba, Shi Guangsheng, mataimakin darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na NPC ya yi bayani kan dalilan da suka sa aka fito da irin wannan kayyadewa. Ya ce,'Irin wannan mataki zai ba da taimako wajen warware muhimman batutuwan da ake matukar bukatar warware su ta hanyar kafa doka, kamar tabbatar da hakkin kadarorin gwamnati da kiyaye tsaron kan kadarorin gwamnati, haka kuma, zai taimakawa wajen samar da karin damar ci gaba da yin gyare-gyare da kyautata tsarin sa ido da kula da kadarorin gwamnatin kasar Sin, zai dace da abubuwan gaskiya.'

Wani batu daban da ya jawo hankali sosai shi ne yadda za a hana yin hasarar kadarorin gwamnati ta hanyar tsara tsari. Game da wannan, shirin dokar ta tanadi tsauraran matakai da dama.

A lokacin da ake nazartar shirin dokar, yawancin shawarwari da mambobin zaunannen kwamitin NPC suka gabatar sun shafi yadda za a hana yin hasarar kadarorin gwamnatin da kuma sa kaimi kan kiyaye darajar kadarorin gwamnatin da samun riba daga yin amfani da su. Zhu Zhigang, darektan kwamitin kula da ayyukan kasafin kudi na NPC shi ne ya gabatar da shawararsa a fannonin, yana ganin cewa,'A takaice dai, wannan doka tana ta samun kyautatuwa bisa gyare-gyaren da ake yi mata. A ganina, an kafa wannan doka ne domin jarraba ayyukan kiyaye darajar kadarorin gwamnatin da samun riba daga yin amfani da su. Dole ne a tsara wani batu dangane da jarraba ayyukan kiyaye darajar kadarorin gwamnatin da samun riba daga yin amfani da su da kuma tsarin yanke hukunci.' (Tasallah)