Yau 25 ga wata da safe, an kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Yuncheng da ke a lardin Shanxi da ke a taskiyar kasar Sin cikin nasara.
Shahararriya 'yar wasan kwallo hannu ta kasar Sin Zhang Weihong ta zama mai mika wutar ta farko. Da misali karfe 8 na safe, bayan an fara mika wutar daga filin Nanfeng na birnin Yuncheng, an mika wutar a titin Hedong da titin Zhouxi da titi mai suna Yanhu, a karshe dai wutar ta isa cibiyar binciken motoci na birnin Yuncheng, kuma tsawon hanyar mika wutar ya kai kilomita 9.8, masu mika wutar 104 sun shiga cikin wannan aiki.
Yau da yamma, za a ci gaba da mika wutar wasannin Olympic na Beijing a garin Pingyao.(Abubakar)
|