Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-25 08:06:47    
Zakaran jebu na farko a tarihin wasannin Olympic na zamanin yau

cri

Kamar yadda kowa ya sani, ko ina ana iya ganin kayayyakin jebu, zakarun jebu na wasannin Olympic su ma haka ne. Amma zakaran jebu na farko a tarihin wasannin Olympic shi ne zakaran gudun marathon a gun zama na 3 na gasar wasannin Olympic ta zamanin yau da aka shirya a birnin St. Louis na kasar Amurka a shekarar 1904.

A gun gasar gudun marathon da aka yi a wancen lokaci, wani 'dan wasa daga kasar Amurka ya yi gudu cikin sauri, daga baya kuma ya ji ciwon kafa, sai ya daina kuma ya shiga motar da aka shirya musamman domin 'yan wasa wadanda ba su iya ci gaba ba. Bayan mintoci da dama, wannan 'dan wasa ya warke, kuma ya fice daga mota saboda 'yan wasa da suka daina gasa sun yi yawan gaske. 'Dan wasan ya koma wurin gasa saboda yana son karban tufafinsa a can, amma ya yi gudu kan hanya cikin sauri kuma ya fi sauran 'yan wasa, shi ya sa 'yan kallon dake bakin hanya sun yi farin ciki kwarai da gaske kuma sun yi ihu saboda ba su san wannan 'dan wasa ya taba daina gudu ba.

A karkashin irin wannan hali, 'dan wasan ya yi la'akari sosai da sosai, daga baya kuma ya tsai da cewa, zai yi amfani da kuskuren 'yan kallo kuma zai ci gaba da yin gudu tare da sauran 'yan wasa wadanda ba su taba daina gudu ba. Yana tsammani cewa, a halin da suke ciki, kuzarin jikinsa ya fi na sauran 'yan wasa saboda ya taba samun hutu a cikin mota, shi ya sa kila zai samu zama na farko.

A karshe dai, ya isa wurin karshe na gasar a gaban sauran 'yan wasa kuma ya zama zakara. 'Yan kallon kasar Amurka sun mayar da shi jarumin al'ummar kasarsu saboda ya samu zama na farko cikin sauki. Daga baya kuma diyar shugaban kasar Amurka na wancen lokaci ta ba shi lambar zinariya.

Amma cikin sauri, wasu mutane sun tarar da cewa, wannan 'dan wasa ya taba samun hutu a cikin mota, kuma sun sanar da kwamitin shirya gasar labarin, a sanadiyar haka, an karbo lambar zinariya daga hannunsa kuma an hore shi. Daga baya kuma an bai wa 'dan wasa wanda ya samu zama na biyu a cikin gasar lambar zinariya.

Bayan shekaru da dama da suka shige, an tarar da cewa, wannan 'dan wasa shi ma zakaran jebu ne. Yayin da yake gudu, ya ji gajiya sosai da sosai, sai malamin koyar da wasa ya ba shi giya domin ya sha kuma ya sa magani mai sa kuzari a ciki. Amma a wancen lokaci, ba a fara hana yin amfani da magani mai sa kuzari ba sai daga shekarar 1960.(Jamila Zhou)