Ran 17 ga wata a birnin Beijing, wani jami'i daga hukumar kula da aikin gandun daji ta kasar Sin ya bayyana cewa, Beijing ya riga ya cika alkawarin dasa bishiyoyin da ya yi a cikin rahoton neman samun iznin shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, kuma aikin ya zarce ma'aunin da aka tsara. Ya zuwa karshen shekarar 2007, fadin bishiya da ciyawa da fure na birnin Beijing ya riga ya wuce kashi 40 cikin dari, fadin bishiya na tsaunuka na birnin ya zarce kashi 70 cikin dari, ban da wannan kuma yawan ranaikun dake cike da iska mai tsabta ya kai kashi 70 a cikin duk tsawon shekara, ana iya cewa, muhallin halittu masu rai da marasa rai ya samu kyautatuwa a bayyane. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.
A shekarun 1950, fadin kungurmin daji na Beijing ya kai kashi 1.3 cikin dari ne kawai, muhallin hallitu masu rai da marasa rai ba shi da kyau. Tun bayan shekarun da suka shige, musamman bayan da aka ci nasarar samun iznin shirya gasar wasannin Olympic a shekarar 2001, birnin Beijing ya dauki matakai a jere domin farfado da kuma kyautata muhallin hallitu masu rai da marasa rai.
A shiyyoyin dake kewayen dakuna da cibiyoyin wasannin Olympic, birnin Beijing ya tabbatar da ayyukan dasa bishiya da ciyawa da kuma fure a jere, alal misali, lambun shan iska na kungurmin daji na Olympic wanda shi ne fili mafi girma da aka gina domin kyautata muhallin hallitu na birnin Beijing, yana ba da babban amfani wajen kayyade iskar gas mai dumaman yanayi da kuma kyautata ingancin ruwa da iska. Direkta mai kula da lambun shan iskar nan Tang Tong ya yi mana bayani cewa, fadin lambun shan iskar ya kai hekta 680, kuma an gina tafkuna da filaye masu damshi a ciki. Ya ce: "Yawan bishiyoyin da aka dasa a cikin wannan lambun shan iska ya kai fiye da dubu 530, sun yi yawan gaske, kuma suna ba da amfani wajen fitar da iska mai tsabta."
Birnin Beijing tana aiwatar da aikin bisa tsarin musamman na shiyya shiyya, game da wannan, shugaban hukumar kula da aikin dasa bishiya ta birnin Beijing Dong Ruilong ya yi mana bayani cewa, a cibiyar birnin, gwamnatin birnin ta bukaci dukkan unguwoyi da gundumomin dake karkashin jagorancinta da su gina babban filin bishiya a kalla 1 ko 2 a kowace shekara, ta haka, masauka birnin za su iya ganin bishiyoyi a ko ina. A karkarar birnin, an dasa gandun daji mai fadin muraba'in hekta dubu 25 domin kare halittu masu rai da masara rai. A tsaunuka kuwa, sassan da abin ya shafa sun rufe tsaunuka domin dasa bishiyoyi, a sanadiyar haka, fadin bishiyoyin wuraren ya kai kashi 95 cikin dari. Dong Ruilong ya ce: "Ya zuwa karshen shekarar bara, fadin bishiyoyin Beijing ya kai kashi 43 cikin dari, fadin gandun daji na tsaunuka na birnin ya kai kashi 70.49 cikin dari, yawan shiyyoyin da aka kafa domin kare albarkatun hallitu ya kai 20, wato fadinsu ya kai 8 cikin dari na duk fadin birnin Beijing. Saboda haka ana iya cewa, Beijing ya riga ya cika alkawarin da ya yi yayin da yake neman samun iznin shirya gasar wasannin Olympic."
A sa'i daya kuma, Beijing yana gudanar da aikin yaki da rairayi tare da sauran jihohin dake kewayensa. Wani jami'i mai kula da aikin na hukumar gandun daji ta kasar Sin Liu Tuo ya ce: "A kan tudun rairayi na jihar Mongolia ta gida dake arewacin Beijing, mu kan yi amfani da ciyawa da kasa mai damshi domin rufe rairayi, da haka za a hana yaduwar hamada." Liu Tuo ya ci gaba da cewa, yanayin iskar kura mai tsanani ya ragu a bayyane a Beijing saboda bishiyoyi suna kara karuwa.(JamilaZhou)
|