Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-24 17:57:09    
Makurdadar Yuantouzhu a tabkin Taihu

cri

Tabkin Taihu na daya daga cikin manyan tabkunan zakin ruwa guda 5 a kasar Sin, yana cikin birnin Wuxi na lardin Jiangsu a gabashin kasar Sin. A arewa maso yammacin gabar wannan tabki, akwai wata makurdada mai suna Yuantouzhu, ma'anar 'Yuan' ita ce kififiya, 'tou' wato kai. Saboda akwai wani babban dutse a cikin tabkin Taihu, kuma siffarsa ta yi kama da kan wani kififiya, wanda ya daga kansa, shi ya sa ake kira wannan makurdada 'Yuantouzhu', wato wata makurdadar da ta yi kama da kan kififiya. Yanzu bari mu yi bulaguro a makurdadar Yuantouzhu mai kyan gani a tabkin Taihu tare.

Masu sauraro, abin da kuke saurara shi ne wata wakar gargajiya da ta taba yaduwa a ko ina a wuraren da ke bakin tabkin Taihu yau da shekaru 50 da suka wuce. Sunanta shi ne jiragen ruwan da ke zirga-zirga a tafkin Taihu. Wannan waka ta siffanta kyan ganin makurdadar Yuantouzhu a tafkin Taihu.

A shekarar 1918 ne aka fara gina manyan lambuna da gidaje a wurin da ke kewayen makurdadar Yuantouzhu. Dattijai da manyan jami'ai da kuma masu kudi sun fara gina lambunansu da manyan gidaje a kusa da makurdadar Yuantouzhu. Bayan da aka fadada shi har tsawon goman shekaru, yanzu fadin wurin yawon shakatawa na makurdadar Yuantouzhu ya kai misalin kadada 300, ya zama daya daga cikin lambuna mafiya girma a kudu da kogin Yangtse.

Makurdadar Yuantouzhu shi ne wuri mafi kyau wajen more ido da ni'imtattun wurare na tabkin Taihu. Ruwa na kewayen wannan babban dutse a bangarorinsa guda 3 a cikin tabkin. In masu yawon shakatawa sun zauna a kan babban dutsen, sai su iya kallon ruwa mai fadi da kuma kananan kwale-kwale a kan tabkin, sai ka ce wani zane irin na gargajiya na kasar Sin.

A ko wace shekara masu yawon shakatawa na gida da na waje fiye da miliyan 3 sun kawo wa makurdadar Yuantouzhu ziyara domin kyan ganinsa.

A wurin yawon shakatawa na makurdadar Yuantouzhu, ana iya ganin manyan duwatsu da tabki mai fadi da kuma kananan kwale-kwalen da ke kan tabkin, haka kuma, ana iya kallon ni'imtattun wurare irin na wuraren da aka fi samun ruwa. Sa'an nan kuma, ana more ido da ni'itattun wurare irin na lambunan da aka samu a wuraren da ke kudu da kogin Yangtse. Kazalika kuma, gine-ginen ba da hidima daga dukkan fannoni da na nishadi da kuma wuraren da mashahuran mutane na zamanin da suka taba kai ziyara da kayayyakin sassaka da zane-zane da rubuce-rubuce irin na gargajiya na kasar Sin da suka samar da kuma almara game da su da dai sauran abubuwan al'adu dukkansu sun sanya wurin yawon shakatawa na makurdadar Yuantouzhu ya shahara bisa ni'imtattun wurare da kuma al'adun mutane.