Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-24 17:45:33    
Birnin Chongqing yana dora muhimmanci kan shigo da kwararru na-gari

cri

A ran 16 ga watan Yuli na shekara ta 1997, wato bayan da birnin Chongqing ya zama birni na hudu da ke karkashin jagorancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye ba da jimawa ba, bisa matsayinsu na 'yan kungiyar ba da hidima ta rukunin farko, Chen Shu da sauran masu digiri dakta 38 sun zo birnin domin raya shi, kuma wannan shi ne wani aiki da birnin Chongqing ya gudanar wajen shigo da kwararru daga hukumomi daban daban na gwamnatin kasar. Bayan da Chen Shu ya yi aiki a birnin har shekara guda, ya tsai da kudurin ci gaba da yin zama a wurin. Kuma ya bayyana cewa, yana son gudanar da aiki a birnin Chongqing har ya yi ritaya, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ya kan ji karfi a wurin, kuma ya kara da cewa, "Bunkasuwar Chongqing ta sa rayukan mutane sosai, shi ba wani birni na kullum ba ne, yana da matukar kyau. Dukkan mutanen kasar Sin da na duniya suna iya gano bunkasuwarsa, sabo da haka kwararru sun kwarara zuwa brinin."

Xie Xin, zaunannen mataimakin shugaban ofishin kula da kwararru na gwamnatin birnin Chongqing ya bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da 10, birnin Chongqing ya shigo da dimbin kwararru na-gari. Kuma ya kara da cewa, "A cikin wadannan shekarun da suka gabata bayan da gwamnatin kasar Sin ta fara shugabantar birnin Chongqing kai tsaye, shigo da kwararru wani muhimmin aiki ne a cikin ayyukanmu wajen kwararru. Musamman ma sabo da ba mu iya horar da wasu kwararru na-gari na salon kirkire-kirkire a cikin gajaren lokaci, shi ya sa muka dauki mataki wajen shigo da kwararru daga sauran birane da kuma ketare. Ta hanyoyi daban daban, mun shigo da kwararru fiye da 800 da ke rike da fasahohi iri daban daban, da kuma masu digiri dakta 290 a fannonin ilmi da sana'o'in da ake bukatarsu sosai. Ban da wannan kuma mun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kwalejin ilmin kimiyya ta kasar Sin domin shigad da cibiyarta ta manhaja cikin birnin."


1 2